Muhammad Sani Abdullahi kuma ana kiransa da Dattijo, ya kasance kwararre ne akan dabarun cigaban ƙasashen duniya kuma ma'aikacin gwamnati ne. Dattijo yayi aiki a matsayin mai bada shawara akan tsare-tsare a ofishin zartarwa na shugaban Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki Moon dake New York kasar Tarayyar Amurka, inda anan ne ya tsare kungiyar da ta samar da Sustainable Development Goals (SDGs).[1][2] Dattijo ya ijiye aikin domin ya dawo yayi aiki a kasar sa Nijeriya, inda ya zama kwamishinan Budget and Planning a karkashin gwamnatin Jihar Kaduna wanda Gwamna Nasir El Rufai ya nada shi.

Muhammad Sani Abdullahi
Rayuwa
Haihuwa Jihar Kaduna, 18 Disamba 1980 (43 shekaru)
ƙasa Najeriya
Karatu
Makaranta Jami'ar Ahmadu Bello
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
Imani
Jam'iyar siyasa All Progressives Congress

Farkon Rayuwa da Karatu

gyara sashe

An haife Sani Abdullahi a Jihar Kaduna, yayi karatun Masters Degree a Development Economics and Policy daga Jami'ar Manchester sannan yasamu yin wani Masters din a Jami'ar Ahmadu Bello a fannin International Affairs and Diplomacy. Yayi karatuttuka da dama certificates wanda ya haɗa da Public Finance daga London School of Economics; Sustainable Development a Jami'ar Columbia da kuma Advanced Project Management a Jami'ar Oxford. Yakasance yana daga cikin 2017 cohort na Jami'ar Georgetown da sukayi Leadership Seminar.[3]

Manazarta

gyara sashe
  1. "World Bank Live". World Bank.
  2. "El-Rufai to appoint Ban ki Moon's special adviser as Kaduna State Commissioner". TheScoop NG. 29 July 2015. Archived from the original on 30 April 2019. Retrieved 10 February 2019. Text "dead-url" ignored (help)
  3. Cite web|url=https://gls.georgetown.edu/sites/gls/files/gls_program_2017_-_update_20171031.pdf%7Ctitle=GLS[permanent dead link] CLASS OF 2017|last=|first=|date=31 October 2017|website=Georgetown University|archive-url=|archive-date=|dead-url=|access-date=