Muhammad Kudu Haruna (22 ga watan Satumban 1951) ɗan jarida ne a Najeriya, marubucin siyasa, shugaba kuma Kwamishinan Zaɓe na INEC tun 2015.[1][2][3] Yana cikin mambobi shida da aka naɗa a matsayin kwamishinan INEC, yana aiwatar da jihohin Kwara, Kogi da Kaduna.[4][5] Ya fara aiki a watan Satumbar 2016.[6]

Muhammad Kudu Haruna
Rayuwa
Haihuwa Ibadan, 22 Satumba 1951 (73 shekaru)
ƙasa Najeriya
Karatu
Makaranta Columbia University (en) Fassara
University of Glasgow (en) Fassara
Sana'a
Sana'a Election Committee (en) Fassara

An haife shi a Ibadan kuma ya fito daga Bida ta tsakiya Najeriya amma ya girma a jihar Kano. Ya yi karatunsa daga shekarar 1957 zuwa 1960 a Tudun Wada Primary School Kano, Makarantar Kuka Kano ya ƙare a shekarar 1964 sannan ya dawo gidansa kuma ya yi babbar takardar shaida a Government College Bida, daga shekarar 1965 zuwa 1968 sannan a 1971 zuwa 1975 ya kammala karatunsa a jami'ar Ahmadu Bello Zariya, Kaduna kuma ya tafi Glosgow College of Technology, Scotland daga 1979 ya kammala a 1980 sannan ya halarci makarantar aikin jarida a Jami'ar Columbia a 1984 kuma a 1995 ya halarci Harvard Advanced Management Programme.[7][8][9][10]

Ya fara aikin jarida ne a kamfanin jaridar New Nigerian Newspapers Company Limited a shekarar 1976 kuma ya zama manajan darakta a shekarar 1989 kuma ya kasance memba kuma shugaban gudanarwa na Mujallar Citizen News a shekarun 90s daga baya a cikin 1998 a jamhuriya ta uku lokacin da Janar Abdulsalami Abubakar ya zama shugaban ƙasa yana mulki. Babban sakataren yaɗa labaransa har zuwa 1999 kuma ya koyar a Jami'ar Ahmadu Bello Zariya a ƙarƙashin sashin sadarwa ta zamani a 2008 zuwa 2014 a matsayin babban malami sannan kuma yana aiki a New Nigerian Today, Gamji, The Nation and Daily Trust tare da New Diary online. Ya kuma yi aiki tare da Majalisar Jarida inda yake gabatar da ƙasidu a kan siyasa, aikin jarida, tarukan ƙarawa juna sani, taron ƙarawa juna sani da cibiyoyi suka shirya da lakcoci sannan yana aiki tare da ƙungiyar Editocin Najeriya da kuma kwamishinonin hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa ya kasance memba na African Centre for Democratic Governance, Technical Kwamitin da ke kula da sayar da hannun jari da kasuwanci a ƙungiyar masu mallakar jaridu ta gidan talabijin na Najeriya ya kuma yi aiki a matsayin darektan Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya, Forte Oil and Conoil da memba kwamitin Vision 2010, Kwamitin hangen nesa 2020 da Bankin Jama'a.[11][7][12]

Kudu Haruna mutum ne na kusa kuma wanda ya fi kowa alaƙa da ƴan wasan siyasa da ƴan wasan kwaikwayo a Najeriya da kuma na tsofaffin ƴan wasan da suka tsara kundin tsarin mulkin 1999 a ƙasar.[3]

Matsayi a kwamitin zaɓe

gyara sashe

Irin waɗannan muƙamai da yake riƙe da su a INEC sun haɗa da[13][14]

  • Shugaban kwamitin binciken da kwamitocin saye kayan aikin fasaha
  • Cigaba da naɗin membobi DA kwamitin ladabtarwa
  • Mambobin kwamitin ayyuka da dabaru na zaɓe
  • Membobin hukumar zaɓe
  • Bayanin memba da kwamitin ilmantar da masu zaɓe
  • Kwamitin kula da lafiya da jin daɗin membobin.

Bayanan kula

gyara sashe
  1. https://blerf.org/index.php/biography/haruna-malam-mohammed-kudu/
  2. https://dailytrust.com/in-celebration-of-mohammed-haruna/
  3. 3.0 3.1 "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2023-03-15. Retrieved 2023-03-15.
  4. https://nggovernorsforum.org/index.php/past-chairmen/82-topics/756-as-buhari-swears-in-6-new-inec-commissioners-28-states-still-without-recs
  5. https://saharareporters.com/2016/12/07/buhari-swears-6-inec-commissioners
  6. https://www.icirnigeria.org/here-are-the-inec-personnel-responsible-for-saturdays-election-postponement/
  7. 7.0 7.1 https://inecnews.com/mallam-mohammed-kudu-haruna-national-commissioner/
  8. https://allafrica.com/stories/201006100538.html
  9. https://inecnigeria.org/
  10. https://books.google.com.ng/books?id=x6Q-AQAAIAAJ&redir_esc=y
  11. "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2023-03-15. Retrieved 2023-03-15.
  12. https://books.google.com.ng/books?id=pJDhAAAAMAAJ&q=Muhammad+Kudu+Haruna+-wikipedia&redir_esc=y
  13. https://inecnigeria.org/
  14. https://punchng.com/2019-inec-promotes-2209-personnel/