Muhammad Garba ɗan jarida ne kuma ɗan Najeriya,[1] kuma ɗan siyasa daga jihar Kano wanda shine kwamishinan yaɗa labarai.[2] kuma memba na Kwamitin Gudanarwa a Ƙungiyar Ƴan Jarida ta Duniya.[3]

Muhammad Garba
Rayuwa
Haihuwa Kano, 25 Nuwamba, 1964 (59 shekaru)
Sana'a
Sana'a ɗan jarida

Rayuwar farko da ilimi gyara sashe

An haifi Muhammad a ranar 22 ga watan Nuwambar 1964 a Yakasai Quarters a Kano Municipal ta jihar Kano. Ya halarci Makarantar Firamare ta Ƙofar Nassarawa da Kwalejin Malamai, Sumaila ya yi Digiri na ɗaya da na biyu a Jami'ar Bayero Kano.[4][5]

Sana'a gyara sashe

Muhammad ya fara aikin jarida a shekarar 1989 tare da Kamfanin Dillancin Labarai na Triumph, Kano a matsayin ɗan jarida kuma ya yi aiki a jihohi daban-daban na tarayya a matsayin wakilin. Daga baya ya girma a cikin aikinsa har ya zama Babban Edita, Editan Labaran Rukuni, da Mataimakin Edita.[4] Ya kuma taɓa zama memba na Hukumar Edita na Jaridun Ƙasa da dama. Muhammed Garba ya riƙe muƙamai daban-daban da suka haɗa da Sakataren Yaɗa Labarai na Mataimakin Shugaban Majalisar Wakilai a shekarar 1993 da Sakataren Yaɗa Labarai na Mataimakin Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje a shekarar 1999 zuwa 2003. Ya fara fafutukar sa na ƙungiyar ne a matsayin shugaban kungiyarsa ta Chapel-The Triumph, wacce ke ƙarƙashin ƙungiyar ƴan jarida ta Najeriya (NUJ), jihar Kano. Daga baya aka zaɓe shi shugaban majalisar jiha na a wa’adi biyu kuma ya kasance mataimakin shugaban ƙungiyar na ƙasa, sannan ya zama shugaban ƙungiyar ƴan jarida ta Najeriya NUJ a shekarar 2009. Muhammad ya kasance shugaban ƙungiyar ƴan jarida ta yammacin Afirka (WAJA) wanda aka zaɓa a Bamako, Mali kuma shine shugaban ƙungiyar ƴan jarida ta Afrika (FAJ) wanda aka zaɓa a Casablanca, Morocco 2009. Muhammad memba ne na Kwamitin Gudanarwa na Ƙungiyar Ƴan Jarida ta Duniya (IFJ) wanda aka zaɓa a Dublin, Ireland. Dr Abdullahi Umar Ganduje ya naɗa Muhammad kwamishinan yaɗa labarai a shekarar 2015.[6][7][8]

Manazarta gyara sashe

  1. https://platinumpost.ng/2020/01/10/profile-muhammad-garba-the-kano-state-government-imagemaker/
  2. https://www.dailytrust.com.ng/kano-ganduje-retains-some-former-commissioners-in-new-cabinet.html
  3. https://thetriumphnews.com/meet-kanos-new-commissioners-i/[permanent dead link]
  4. 4.0 4.1 "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2020-12-03. Retrieved 2021-05-20.
  5. https://platinumpost.ng/2020/03/02/the-journey-of-a-versatile-journalist-to-the-peak/
  6. https://www.kanostate.gov.ng/?q=portfolio/ministry-information-internal-affairs Archived 2021-05-20 at the Wayback Machine
  7. https://guardian.ng/news/kwankwaso-others-made-gandujes-commissioners-list/
  8. https://dailypost.ng/2019/11/05/ganduje-swears-in-new-commissioners/