Mudashiru Obasa
Mudashiru Ajayi Obasa (an haife shi 11 ga watan Nuwamban 1972) lauya ne a Najeriya kuma ɗan siyasa wanda ya yi aiki a matsayin kakakin majalisar dokokin jihar Legas tun shekarar 2015.[1]
Mudashiru Obasa | |||
---|---|---|---|
11 ga Yuni, 2019 - 11 ga Yuni, 2023 District: Agege I (en) | |||
Rayuwa | |||
Haihuwa | Agege, 11 Nuwamba, 1972 (52 shekaru) | ||
ƙasa | Najeriya | ||
Mazauni | Lagos, | ||
Harshen uwa | Yarbanci | ||
Karatu | |||
Makaranta | Jami'ar, Jihar Lagos | ||
Harsuna | Turanci | ||
Sana'a | |||
Sana'a | ɗan siyasa da Lauya | ||
Imani | |||
Jam'iyar siyasa | All Progressives Congress |
Ɗan jam'iyyar All Progressives Congress ne wadda ke mulki.
Rayuwar farko
gyara sasheAn haifi Mudashiru Ajayi Obasa a Agege, wani gari dake jihar Legas kudu maso yammacin Najeriya a ranar 11 ga watan Nuwamban 1972.[2] Ya yi karatun firamare a St Thomas Acquinas Pry School, Surulere, Legas kafin ya wuce Archbishop Aggey Memorial Secondary School, Mushin, Ilasamaja, Legas inda ya samu takardar shedar makarantar West Africa.[3] Ya sami digiri na farko a fannin shari'a a Jami'ar Jihar Legas dake Legas a shekarar 2006.[4]
Sana'ar siyasa
gyara sasheA shekarar 1999 ya tsaya takarar kansila a ƙaramar hukumar Agege a ƙarƙashin jam’iyyar Alliance for Democracy kuma ya yi nasara. Ya yi aiki tsakanin 1999 zuwa 2002.[5]
An zaɓe shi ɗan majalisar dokokin jihar Legas mai wakiltar mazaɓar Agege I a shekarar 2007. An sake zaɓen shi a 2011, 2015 da 2019.[6][7]
A cikin shirin na #EndSARS a jiharsa, an yi masa wani bidiyo kai tsaye a gidan talabijin yana cewa " LSHA ba za ta amince da mutuwar ƴan ta'adda a hannun rundunar ƴan sanda ba" a lokacin da yake kira da a yi shiru na minti ɗaya aya ga waɗanda rikicin #Lekki ya shafa. da sauran su a faɗin Najeriya.[8]
Cin hanci da rashawa
gyara sasheA shekarar 2020 ne dai jaridar Sahara Reporters ta ruwaito ta fitar da rahoton zargin almubazzaranci da dukiyar al’umma da ake yi masa. Sai dai ya musanta dukkan zarge-zargen.[9][10][11][12]
Daga baya Sahara Reporters ta ruwaito cewa hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arziƙin ƙasa zagon ƙasa ta kai Obasa domin yi masa tambayoyi a ranakun 8 da 9 ga Oktoban 2020. A cewar wata majiya mai tushe ta tabbatarwa da Sahara Reporters cewa Obasa ya nuna rashin lafiya ne a lokacin da ake yi masa tambayoyi a ofishin EFCC, wanda ya sa aka dakatar da tambayoyi. Sai da aka kai Obasa zuwa majinyata na ofishin EFCC kafin a bayar da belinsa.[13] Daga nan Obasa ya nemi a dawo masa da fasfo ɗinsa, wai don neman magani a ƙasashen waje kafin ya tafi Umrah don ganawa da Bola Tinubu a Saudiyya. EFCC na ci gaba da binciken Obasa bisa zargin almundahana da zamba.[14]
Manazarta
gyara sashe- ↑ https://thenewsnigeria.com.ng/2015/06/23/meet-obasa-the-new-lagos-speaker/
- ↑ https://www.legit.ng/456274-the-rise-and-rise-of-the-new-lagos-speaker.html
- ↑ http://encomium.ng/why-i-want-to-come-back-to-house-for-the-fourth-time-hon-mudashiru-obasa/
- ↑ https://www.legit.ng/456274-the-rise-and-rise-of-the-new-lagos-speaker.html
- ↑ http://encomium.ng/profiles-of-the-new-principal-officers-of-lagos-house-of-assembly/
- ↑ https://punchng.com/breaking-lagos-speaker-obasa-other-win-lagos-house-of-assembly-seats-in-agege/
- ↑ "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2023-03-16. Retrieved 2023-03-16.
- ↑ https://allnews.ng/news/endsars-we-won-t-honour-miscreants-killed-by-the-police-lagos-speaker-video
- ↑ "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2023-03-16. Retrieved 2023-03-16.
- ↑ https://saharareporters.com/2020/05/15/exclusive-lagos-assembly-speaker-obasa-approves-n258m-printing-invitation-cards-house
- ↑ https://saharareporters.com/2020/05/04/exclusive-how-obasa%E2%80%99s-wife-receives-n10m-illegal-monthly-allocation-lagos-assembly
- ↑ https://guardian.ng/tag/mudashiru-obasa/
- ↑ https://saharareporters.com/2020/10/10/exclusive-lagos-assembly-speaker-obasa-returns-efcc-interrogation-feigns-sickness
- ↑ https://saharareporters.com/2021/05/11/lagos-speaker-obasa-under-efcc-probe-sighted-mecca-after-lying-he-was-sick-needed-his