Monisade Afuye
Mataimakiyar Gwamnan jahar Ekiti
Monisade Christiana Afuye (an haife ta 28 ga watan Satumban 1958)[1] ƴar siyasar Najeriya ce wadda ta zama mataimakiyar gwamnan jihar Ekiti tun shekarar 2022.[2]
Monisade Afuye | |||
---|---|---|---|
16 Oktoba 2022 - ← Bisi Egbeyemi (en) | |||
Rayuwa | |||
Haihuwa | Ikere, 28 Satumba 1958 (66 shekaru) | ||
ƙasa | Najeriya | ||
Harshen uwa | Yarbanci | ||
Karatu | |||
Harsuna |
Turanci Yarbanci Pidgin na Najeriya | ||
Sana'a | |||
Sana'a | ɗan siyasa da entrepreneur (en) | ||
Imani | |||
Addini | Kiristanci | ||
Jam'iyar siyasa | All Progressives Congress |
Tarihin Rayuwa
gyara sasheAn haifi Monisade Christiana Afuye a ranar 28 ga watan Satumban 1958 a Ikere-Ekiti, ƙaramar hukumar Ikere. Ta yi karatun firamare a Saint Joseph CAC Primary School Aramoko, Aramoko Ekiti, sannan ta yi karatun sakandare a makarantar Amoye Grammar School, Ikere-Ekiti. Ta samu difloma ta al'ada da babbar difloma a fannin harkokin gwamnati daga Crown Polytechnic, Ado Ekiti, jihar Ekiti.[1]