Moncef Ben Salem
Moncef Ben Salem ( Tunisian Arabic; Fabrairu 1, 1953 - Maris 24, 2015) ɗan siyasan Tunisiya ne kuma malamin jami'a. [1] [2] Ya taɓa zama ministan ilimi mai zurfi da bincike na Kimiya a karkashin firaminista Hamadi Jebali. [3]
Moncef Ben Salem | |||||||
---|---|---|---|---|---|---|---|
24 Disamba 2011 - 29 ga Janairu, 2014
22 Nuwamba, 2011 - 28 ga Faburairu, 2012 District: Q16670951 Election: 2011 Tunisian Constituent Assembly election (en)
| |||||||
Rayuwa | |||||||
Haihuwa | 1 ga Afirilu, 1953 | ||||||
ƙasa |
French protectorate of Tunisia (en) Tunisiya | ||||||
Mutuwa | 24 ga Maris, 2015 | ||||||
Karatu | |||||||
Makaranta | University of Toulouse (en) | ||||||
Sana'a | |||||||
Sana'a | masanin lissafi, ɗan siyasa da Malami | ||||||
Employers | University of Maryland (en) | ||||||
Imani | |||||||
Addini | Musulunci | ||||||
Jam'iyar siyasa | Ennahda Movement (en) |
Tarihin Rayuwa
gyara sasheRayuwar farko
gyara sasheAn haifi Moncef Ben Salem a ranar 1 ga watan Afrilu 1953. Ya sami digiri na BA a fannin lissafi da Physics a shekarar 1972 sannan ya yi digiri na biyu a fannin lissafi a shekarar 1974.[4][5][6] Ya sami digirin digirgir a fannin lissafi da Physics daga Jami'ar Toulouse da Supméca a birnin Paris.[4][5][6] Ya kasance memba na Ƙungiyar Union of Arab Mathematicians and Physicians daga shekarun 1980 zuwa 1987. Shi ne ya kafa Ecole Nationale d'Ingénieurs de Sfax a cikin shekarar 1983[7]
Harkar siyasa da aiki
gyara sasheYa kasance ɗan ƙungiyar Ennahda Movement. Ya yi suka ga shugabannin Habib Bourguiba da Zine El Abidine Ben Ali, yana mai kiran Bourguiba a matsayin "Zionist". Sakamakon gwagwarmayar siyasarsa ƙarƙashin Ben Ali, an daure shi na tsawon watanni goma sha takwas daga shekarun 1987 zuwa 1989, kuma daga shekarun 1990 zuwa 1993. A shekarar 1987, an soke fasfo ɗinsa, kuma an hana shi fita daga Tunisia ko tafiya cikin kasar tsawon shekaru ashirin, kamar yadda 'ya'yansa suka yi.[4][8][9] Daga shekarun 1993 zuwa 2011, an tilasta masa zama a ƙarƙashin sa ido (Surveillance). An kuma hana shi aiki a matsayin malamin jami'a. A lokacin waɗancan shekarun, an tallafa masa da Kwamitin Masana'antu da kuma al'ummar ilmin lissafi na Amurka. Daga baya ya koyar a Jami'ar Maryland da ke Amurka, a Cibiyar Nazarin Kimiyya ta Faransa a Faransa, Italiya, Jamus, Belgium, da Jami'ar Sfax da ke Tunisiya.
Minista
gyara sasheA ranar 20 ga watan Disamba, 2011, bayan an hambarar da tsohon shugaban ƙasa Ben Ali, ya shiga majalisar ministocin Jebali a matsayin ministan ilimi mai zurfi. [6]
Mutuwa
gyara sasheYa rasu a ranar 24 ga watan Maris, 2015, ya bar bazawara da ‘ya’ya 4.[4][10][11]
Manazarta
gyara sashe- ↑ (in French) Babnet Dec'24th 2011
- ↑ [1] leaders.com: Moncef is named a professor again
- ↑ CIA World Leaders
- ↑ 4.0 4.1 4.2 4.3 Cite error: Invalid
<ref>
tag; no text was provided for refs namedleaders
- ↑ 5.0 5.1 Cite error: Invalid
<ref>
tag; no text was provided for refs namedagence
- ↑ 6.0 6.1 6.2 Dr. Moncef Ben Salem to visit the Fields Institute, Fields Institute, 20 March 2012
- ↑ "Moncef Ben Salem nommé professeur de l'enseignement supérieur". Leaders (in Faransanci). Retrieved 2017-11-16.
- ↑ (in French) Death of Moncef Ben Salem Business News March 24, 2015
- ↑ [2] (in Larabci)
- ↑ (in French) Death of Moncef Ben Salem Business News March 24, 2015
- ↑ [3] (in Larabci)