Mohammad-Ali Rajai
Mohammad-Ali Rajai an haifeshi ranar 15 ga watan Yunin Shekarar 1933 kuma ya mutu a ranar 30 ga watan Agustan shekara 1981, shine shugaban kasar Iran daga 2 zuwa 30 ga watan Augustan shekarar 1981, bayan daya gama mukaminsa na firayim minista a karkashin gwamnatin Abolhassan Banisadr. Bugu da kari kuma shine minista mai kula da harkokin waje na kasar iran daga ranar 11 ga watan maris shekara ta 1981 zuwa 15 ga watan Agustan shekarar 1981. Anyi kai masa hari da Bom a ranar 30 ga watan Agustan 1981 tare da firayim minista dinshi wanda hakan yayi sanadiyyar mutuwar shi.
Mohammad-Ali Rajai | |||||||||
---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|
2 ga Augusta, 1981 - 30 ga Augusta, 1981 ← Abolhassan Banisadr - Ali Khamenei →
11 ga Maris, 1981 - 15 ga Augusta, 1981 ← Karim Khodapanahi (en) - Mir-Hossein Mousavi (en) →
12 ga Augusta, 1980 - 4 ga Augusta, 1981 ← Mehdi Bazargan (en) - Mohammad-Javad Bahonar (en) →
28 Mayu 1980 - 1 ga Augusta, 1981 District: Tehran, Rey, Shemiranat and Eslamshahr (en) | |||||||||
Rayuwa | |||||||||
Haihuwa | Qazvin (en) , 15 ga Yuni, 1933 | ||||||||
ƙasa | Iran | ||||||||
Mutuwa | Tehran, 30 ga Augusta, 1981 | ||||||||
Makwanci | Hafte Tir Mausoleum (en) | ||||||||
Yanayin mutuwa | kisan kai (explosive device (en) ) | ||||||||
Killed by | Massoud Keshmiri (en) | ||||||||
Karatu | |||||||||
Makaranta | Kharazmi University (en) | ||||||||
Harsuna | Farisawa | ||||||||
Sana'a | |||||||||
Sana'a | ɗan siyasa da Malami | ||||||||
Imani | |||||||||
Addini | Shi'a | ||||||||
Jam'iyar siyasa | Islamic Republican Party (en) | ||||||||
Farkon Rayuwa da karatun shi
gyara sasheAn haifi Mohammad-Ali Rajai a ranar 15 ga watan Yunin 1933 a garin Qazvin dake akasar iran.[1] Mahaifin shi dan tireda ne mai shago daya rasu tun Mohammad-Ali Rajai yana dan shekara hudu[2][3] Rajai ya girma a Qazvin wanda daga bisani ya koma Tehran a karshen shekarar 1940. Kuma ya shiga kungiyar SOjan sama ta kasar Iran a lokacin yana dan shekara 16-17[4][5][6]
Siyasarshi
gyara sasheKafin juyin musulunci
Bayan komawa Tehran Rajai ya kasance ya kasance cikin masu kishiyartar Gwamnatin Shah, a cikin kungiyar Mahmoud Taleghani da kuma Fadaeian group. A lokaci guda kuma babban memba a fitattaciyar kungiyar nan People's Mujahedin of Iran (MKO). A shekarar 1960 Rajai ya shiga kungiyar kare yanci ta Iran wato Freedom Movement of Iran.[7][8] Saboda yawan kalubalantar Gwamnatin shah, Jamian sharo sun kamashi har sau biyu, kuma ya bayyana irin ukubar daya fuskanta daga jami'an tsaro a dalilin hakan. Daya daga cikin kamun da yafi dadewa a hannun jami'an tsaro shine daga May 1974 har zuwa jarshen shekarar 1978.
Bayan juyin Musulunci
Rajai yana cikin yan gaba gaba a lokacin yunkurin tabbatar da gwamnatin musulunci, shine shugaban masu ra'ayin dakile tasirun Amurka a jami'o'in iran, wanda yasa ake kiran wannan yunkuri da Cultural Revolution. Rajai ya rike manyan wurare a Gwamnatin Iran iran bayan an tabbatar da Gwamnatin musulunci. Ayyukan da yayi sun hada da;
- Ministan Ilimi
- Masu takarar kasancewa cikin Islamic Consultative Assembly
- Firayim Minista
- Shugaban Kasa
Ministan Ilimi
gyara sasheDa farko Gholam Hosein Shokohi shine Ministan ilimi na Iran shi kuma Rajai ya kasance daya daga cikin mukarraban shi, amma daga bisani Shokohi ya ajiye aiki a sakamakon rashin lafiyar da yake fama da ita, shi kuma Muhammad Rajai sai aka nadashi a matsayin mai kula da ayyukan Ministiri gaba daya. A karshe dai Mehdi Bazargan ya gabatar dashi a matsayin minista
Manazarta
gyara sashe- ↑ https://books.google.com.ng/books?id=JJEIQbUnGyYC&pg=PA228&redir_esc=y
- ↑ Brown, Roland Elliott (20 April 2017). "Rajai: The Clerics' Loyalist (1981)". IranWire
- ↑ http://iricenter.org/uncategorized/documentary-biography-of-president-mohammad-ali-rajai/
- ↑ https://www.britannica.com/biography/Mohammad-Ali-Rajai
- ↑ Kihss, Peter (1 September 1981). "Obituaries | Mohammad Ali Rajai, Iran's President". New York Times. Archived from the original on 24 May 2015.
- ↑ Brown, Roland Elliott (20 April 2017). "Rajai: The Clerics' Loyalist (1981)". IranWire.
- ↑ Houchang E. Chehabi (1990). Iranian Politics and Religious Modernism: The Liberation Movement of Iran Under the Shah and Khomeini. I.B.Tauris. p. 87. ISBN 978-1-85043-198-5. Retrieved 27 August 2013.
- ↑ "Mohammad Ali Raja'i". Encyclopædia Britannica. Retrieved 27 August 2013.