Mansur Mukhtar (an haife shi a ranar 21 ga watan Satumban 1959) masanin tattalin arziƙin Najeriya ne wanda aka naɗa shi ministan kuɗi a majalisar ministocin shugaba Umaru Musa Ƴar'Adua a ranar 17 ga Disambar 2008.[1] Ya bar mulki a watan Maris ɗin 2010 lokacin da muƙaddashin shugaban ƙasa Goodluck Jonathan ya rusa majalisar ministocinsa.[2]

Mansur Mukhtar
Ministan Albarkatun kasa

17 Disamba 2008 - 17 ga Maris, 2010
Shamsuddeen Usman - Olusegun Olutoyin Aganga
Rayuwa
Haihuwa jahar Kano, 21 Satumba 1959 (65 shekaru)
ƙasa Najeriya
Karatu
Makaranta University of Sussex (en) Fassara
King's College, Lagos
Thesis The dynamics of agricultural development in Nigeria : a critical assessment of radical political economy perspectives and a case study of groundnut producers
Sana'a
Sana'a Mai tattala arziki

An haifi Mukhtar a ranar 21 ga watan Satumban 1959 a garin Kano. Ya halarci Kwalejin King da ke Legas, sannan ya yi karatun digiri na biyu a Jami’ar Ahmadu Bello Zariya. Tattalin Arziƙi shekarar 1980.

Ya yi aiki a Babban Bankin Najeriya a matsayin Mataimakin Masanin Tattalin Arziƙi (1980-81), kuma a matsayin mataimakin malami mai digiri, a 1981 da 1982 a Jami'ar Bayero dake Kano. Ya sami digiri na biyu a fannin tattalin arziƙi da siyasa na ci gaba daga Jami'ar Cambridge, United Kingdom a shekarar 1983, sannan ya sami digiri na uku a fannin tattalin arziƙi daga Jami'ar Sussex, Brighton a cikin Fabrairun 1988. Mukhtar ya kasance shugaban sashin tattalin arziƙi kuma malami a jami'ar Bayero ta Kano daga 1988 zuwa 1990.[3]

Muhtar ya kasance mai bada shawara/mataimaki na musamman ga ministan noma da albarkatun ƙasa daga 1990 zuwa 1992. Ya yi aiki a Bankin Duniya (1992-2000) a ayyuka daban-daban. Ya kasance mataimakin babban manaja a bankin United Bank for Africa tsakanin watan Yulin 2000 zuwa Maris 2001, sannan ya zama babban darakta a bankin ci gaban Afirka da ke Tunis.[3]

An naɗa shi ministan kuɗi a majalisar ministocin shugaba Umaru Musa Ƴar’adua a ranar 17 ga watan Disambar 2008.

Mukhtar ya kasance babban daraktan bankin duniya daga 2011 zuwa 2014. [4] Naɗin da ya yi a kan wannan matsayi na cikakken lokaci a birnin Washington ya samo asali ne sakamakon samar da karin kujera ga Afirka a cikin kwamitin bankin duniya . Yanzu Afirka na da kujeru uku a hukumar tun watan Nuwamban shekarar 2010. Ayyukan Dokta Mansur a cikin hukumar za su haɗa da tsara dabaru da kuma amincewa da manufofi da shirye-shiryen ƙungiyar Bankin Duniya a ƙasashe mambobin ƙungiyar, amincewa da manufofin cikin gida da suka haɗa da albarkatun ɗan adam da sa ido kan al'amuran da suka shafi gudanar da ayyukan ƙungiyar.[5]

A shekarar 2014 ya koma Jeddah a ƙasar Saudiyya inda ya zama mataimakin shugaban ƙasa na ayyukan bankin ci gaban Musulunci.[4]

Manazarta

gyara sashe