Kennedy Kwasi Kankam
Kennedy Kwasi Kankam dan siyasan Ghana ne kuma dan majalisar dokoki ta bakwai na jamhuriyar Ghana ta hudu mai wakiltar mazabar Nhyiaeso a yankin Ashanti akan tikitin New Patriotic Party.[1][2][3][4] A halin yanzu shi ne shugaban karamar hukumar Asokore Mampong Municipal.[5]
Kennedy Kwasi Kankam | |||
---|---|---|---|
7 ga Janairu, 2017 - 6 ga Janairu, 2021 District: Nhyiaeso Constituency (en) Election: 2016 Ghanaian general election (en) | |||
Rayuwa | |||
Haihuwa | Kumasi, 22 ga Janairu, 1978 (46 shekaru) | ||
ƙasa | Ghana | ||
Harshen uwa | Yaren Asante | ||
Karatu | |||
Makaranta |
Jami'ar Oxford diploma (en) : Effective Writing (en) Kwalejin Prempeh (Satumba 1995 - Nuwamba, 1997) Kwalejin Jami'ar Kirista (2009 - 2013) Bachelor of Arts (en) : business administration (en) Kwame Nkrumah University of Science and Technology (2014 - 2016) Master of Arts (en) : business administration (en) | ||
Harsuna |
Turanci Yaren Asante Harshen Ga Harshen Kasena | ||
Sana'a | |||
Sana'a | ɗan siyasa, accountant (en) , managing director (en) da manager (en) | ||
Wurin aiki | Kumasi | ||
Imani | |||
Addini | Pentecostalism (en) | ||
Jam'iyar siyasa | New Patriotic Party |
Rayuwar farko da ilimi
gyara sasheAn haifi Kankam a ranar 22 ga Janairun shekarar 1978 kuma ya fito daga Adiebeba a yankin Ashanti na Ghana. Ya yi karatun sa na farko a makarantar Nhyiaeso International School da ke Kumasi daga Yuli 1982 zuwa Yulin shekara ta 1994. Ya kuma halarci Kwalejin Prempeh daga Satumba 1995 zuwa Nuwamban shekarar 1997. Daga nan kuma ya tafi jami’ar Christian Service College inda ya kammala digirinsa na farko a fannin harkokin mulki daga shekarar 2009 zuwa 2013. Daga nan ya tafi KNUST inda ya yi digirinsa na biyu a fannin Accounting daga shekarar 2014 zuwa 2016. Ya kara zuwa Jami'ar Oxford don samun difloma a fannin rubutu mai inganci a watan Satumba na 2017.[6][7]
Aiki
gyara sasheKankam shi ne Manajan Darakta na Kamfanin Kekka Limited tun shekara ta 2005. Ya kasance Mataimakin Manajan Gudanarwa na Metro Mass Transit Limited daga shekarar 2002 zuwa 2004. Ya kasance manajan tallace-tallace na Nick and Cilogar Investment Limited.[7] Shi ne kyaftin na Kumasi Royal Golf Club na yanzu.[8]
Siyasa
gyara sasheKankam memba na New Patriotic Party ne kuma tsohon dan majalisa mai wakiltar mazabar Nhyiaeso.[9][10][11] A watan Yunin shekarar 2020, ya rasa kujerarsa ta dan majalisa a hannun Stephen Amoah a lokacin zaben fidda gwani na majalisar dokokin NPP.[12][13][14] Nana Akufo-Addo ne ya zabe shi kuma a halin yanzu shi ne shugaban karamar hukumar Asokore Mampong a yankin Ashanti.[8][15][16]
Kwamitoci
gyara sasheKankam ya kasance mamba a kwamitin kula da asusun jama’a sannan kuma mamba a kwamitin muhalli, kimiya da fasaha.[7]
Rayuwa ta sirri
gyara sasheKankam Kirista ne.[6] Yayi aure. Yana jin daɗin wasan golf da kallon ƙwallon ƙafa.[7]
Rigima
gyara sasheA watan Yunin shekara ta 2021, babban mai binciken kudi ya umurci Kankam da ya kwato kusan cedi na Ghana 500,000 wanda ya baiwa sama da mutane 300 a mazabar Nhyiaeso. An yi zargin cewa kudaden sun fita ne a matsayin rance amma ba a dawo da su ba.[14][17][18]
Tallafawa
gyara sasheA watan Agustan shekara ta 2019, Kankam ya ba da kyautar motar bas mai kujeru 33 sannan kuma ya yi hayar ofishin jam’iyyar NPP a mazabarsa.[19][20]
Manazarta
gyara sashe- ↑ "Parliament of Ghana".
- ↑ "NPP retains Nhyiaeso seat – Today Newspaper" (in Turanci). Retrieved 2020-12-26.[permanent dead link]
- ↑ FM, Peace. "Parliament - Nhyiaeso Constituency Election 2020 Results". Ghana Elections - Peace FM. Retrieved 2020-12-26.
- ↑ "Ghana MPs - MP Details - Kankam, Kennedy Kwasi". www.ghanamps.com. Retrieved 2020-12-26.
- ↑ "Sam Pyne, Kennedy Kankam confirmed as MCEs - Asaase Radio" (in Turanci). 2021-10-05. Retrieved 2022-08-27.
- ↑ 6.0 6.1 "Kankam, Kennedy Kwasi". Ghana MPS (in Turanci). Retrieved 2022-08-27.
- ↑ 7.0 7.1 7.2 7.3 "Profile Of Asokore Mampong MCE Nominee Hon. Kennedy Kankam". Kessben Online (in Turanci). Retrieved 2022-08-27.
- ↑ 8.0 8.1 "Kennedy Kankam makes history at Asokore Mampong". Modern Ghana (in Turanci). Retrieved 2022-08-27.
- ↑ "Kennedy Kankam's nomination as Asokore Mampong MCE dangerous for NDC – Alhaji Sani". GhanaWeb (in Turanci). 2021-09-20. Archived from the original on 2022-08-27. Retrieved 2022-08-27.
- ↑ "Kennedy Kankam did no wrong with common fund; KMA answered audit queries". Graphic Online (in Turanci). Retrieved 2022-08-27.
- ↑ "NPP primaries: Deputy Speaker, Majority Leader, 12 others go unopposed - MyJoyOnline.com". www.myjoyonline.com (in Turanci). 2020-03-10. Retrieved 2022-08-27.
- ↑ "Kankam, Obour lead movement for Nana Addo re-election". Graphic Online (in Turanci). Retrieved 2022-08-27.
- ↑ "Kankam, Obour lead movement for Nana Addo re-election". Graphic Online (in Turanci). Retrieved 2022-08-27.
- ↑ 14.0 14.1 "Aspiring KMA Mayor, Kennedy Kankam indicted for dishing out Common Fund cash as loans". Citinewsroom - Comprehensive News in Ghana (in Turanci). 2021-06-13. Retrieved 2022-08-27.
- ↑ "'He is not one of us' - Kennedy Kankam's nomination receives strong contention from residents - MyJoyOnline.com". www.myjoyonline.com (in Turanci). 2021-09-20. Retrieved 2022-08-27.
- ↑ Amoh, Emmanuel Kwame (2021-09-20). "Kennedy Kankam's nomination as Asokore Mampong MCE dangerous for NDC - Alhaji Sani". 3News.com (in Turanci). Archived from the original on 2022-08-27. Retrieved 2022-08-27.
- ↑ "Auditor General indicts former Nhyieso MP over failure to recover ¢500k of Assembly's Common Fund - MyJoyOnline.com". www.myjoyonline.com (in Turanci). 2021-06-14. Retrieved 2022-08-27.
- ↑ admin (2021-06-15). "Kennedy Kankam indicted in AG's report". Ghanaian Times (in Turanci). Retrieved 2022-08-27.
- ↑ "Nhyiaeso MP donates bus to constituency". Graphic Online (in Turanci). Retrieved 2022-08-27.
- ↑ "A/R: Nhyiaeso MP purchases bus, rents office for constituents". Modern Ghana (in Turanci). Retrieved 2022-08-27.