Katanga, Najeriya
Katangar gabari birni ne, da ke a jihar Jigawa ta Najeriya. Yana da nisan kilomita 20 daga Kiyawa da kuma nisan 13km daga Dutse babban birnin jihar Jigawa.
Katanga, Najeriya | ||||
---|---|---|---|---|
| ||||
Wuri | ||||
| ||||
Ƴantacciyar ƙasa | Najeriya | |||
Jihohin Najeriya | Jihar Jigawa | |||
Labarin ƙasa | ||||
Yawan fili | 1.3 km² | |||
Bayanan Tuntuɓa | ||||
Kasancewa a yanki na lokaci |
Taswira
gyara sasheYana cikin yankin Kaduna. Babban birnin Kaduna Kaduna (Kaduna) kusan nisan kilomita 141 da garin Katanga. Tashi daga Katanga zuwa Abuja babban birnin Najeriya (Abuja) kusan nisan kilomita 118 ne km/73 .[1] Garin yana da jimillar yawan mutane 7000.
Mutanen Katanga
gyara sasheYawancin mutanen Katanga Hausawa ne. Kusan kashi 90% na al'ummar Hausawa ne, kashi 7.5% Fulani ne, kashi 2.5% na Kanuri .
Noma a Katanga
gyara sasheGarin Katanga na ɗaya daga cikin garuruwa masu samar da abinci ba a jihar Jigawa kaɗai ba har ma a duk fadin Najeriya. A lokacin damina ana samun mutanen Katanga suna shuka amfanin gona kamar gero, masara, shinkafa, gyaɗa, wake, da masara. A lokacin rani manoma a Katanga suna kan hanyarsu ta zuwa tafki don ban ruwa da shuka kankana, tumatur, borkono da alkama.
Manazarta
gyara sashe- ↑ "Katanga, Nigeria - Facts and information on Katanga - Nigeria.Places-in-the-world.com". nigeria.places-in-the-world.com. Retrieved 2022-11-14.