Kasuwar Kurmi

tsohuwar kasuwa a Kano, Najeriya

Kasuwar Kurmi babbar kasuwa ce a cikin birnin Kano, Jihar Kano, Najeriya . Muhammad Rumfa, Sarkin Kano ne ya kafa ta, a karni na Sha biyar 15, kuma har yanzu a karni na ashirin da daya 21 ana amfani da ita. Ya zuwa shekarar dubu biyu da uku 2003, Sale Ayagi shi ne shugaban kungiyoyin kwadago na kasuwar.

Kasuwar Kurmi

Wuri
Map
 12°00′N 8°31′E / 12°N 8.52°E / 12; 8.52
Ƴantacciyar ƙasaNajeriya
Jihajihar Kano
Birnijahar Kano
Yawan mutane
Harshen gwamnati Turanci
Bayanan Tuntuɓa
Kasancewa a yanki na lokaci
Kayan turaren wuta a Kasuwar Kurmi.

Kasuwar Kurmi ta ba da sunan kungiyar kwallon kafa.

An kafa kasuwar Kurmi a cikin karni na goma sha biyar (15) a matsayin cibiyar kasuwanci da adana kayayyaki don cigaban kasuwanci a cikin birni, sakamakon fadada kasuwancin yanki da Sahara. An Kuma gina ta a cikin gundumar Jakara na cikin birni. A lokacin ci gabanta, Kano ta zama cibiyar yanki na kasuwancin kayan gona tare da masana'antun aiki a saka da rinin Zane da yin fata da samar da tukwane. Wannan ya bayar da gudummawa ga jan hankalin garin ga 'yan kasuwa masu yawo daga Yammacin Sudan da Tripoli da Ghadames wanda ya zo sayen kaya. Kafin zamanin mulkin mallaka, an tsara tsarin kasuwar a cikin sifa hudu tare da rumfar rumbu suna yin layi kamar titi mara tsari; a cikin kasuwar, kebabbun wurare da ke ba da samfuran daban daban kuma cinikin shanu yana cikin bangarorin yamma da gefen kasuwar. Kasuwar mutane ne ke kula da ita wadanda ke kula da takamaiman wuraren zama ko samar da sassan. [1]

Kafin Mulkin mallaka da kuma bayan mulkin mallaka

gyara sashe

A cikin a shekarar dubu daya da dari tara da hudu 1904, tsohuwar kasuwa ta rushe kuma aka gina sabuwar ta don inganta hanyoyin samar da kudaden shiga ga jama'a. An bude sabuwar kasuwar a shekarar dubu daya da dari tara da tara 1909, kuma an gina ta da rumfuna guda Dari bakwai da hamsin da biyar 755 da aka yi da yumbu. hakanan kuma yana da masallaci da kotu. A cikin shekarun da suka gabata an samu cigaba na kari, an fadada tituna kuma an nemi wasu masu sayar da dabbobi da su yi kaura. Kewayen kasuwar, musamman yankin Jakara su ma sun shaida fadada cigaba. Koyaya, alkiblar ciniki ta canza daga makwabtan birni na arewa da kasuwancin Saharar zuwa ciniki tare da makwabta na Kudu da Turawa.

A shekarar dubu daya da dari tara da sittin da tara 1969, harkar kasuwar ta fada hannun Karamar Hukumar Kano. Tun daga wannan lokacin, Karamar Hukumar ta karfafa kasuwanni na musamman a cikin gari kamar kasuwar 'Yankaba na kayan lambu da Kasuwar Kantin Kwari na kayan Masaku. Wasu 'Yan kasuwar kuma sun koma sabbin cibiyoyin bunkasa biranen kamar Fagge da kasuwar Sabon Gari. A halin yanzu, kasuwar ta rasa wasu ƙa'idojinta a matsayinta na cibiyar kasuwancin yankin, kuma tana ba da yawancin bukatun masarufin gida. [1]

Manazarta

gyara sashe
  •  Gaba-gaba cikin mayan kasuwanni a Kano, Fitacciyar Kasuwar Kurmi mai fadi ce amma ba tare da lunguna wanda mutum zai iya dacewa cikin sauki. Sassan tanada kananan kantuna, kananan hanyoyin tafiya da kuma. A cikin ciniki, kiyaye kudin da aka karda kuna shirye da ku biya tareda neman ragi, ba abin da suka fada ba. A kai a kai, zaku samu dama a wannan lokacin har ku bayar da abin da kuka samo. ba kowace shakka. [2]

Hanyoyin haɗin waje

gyara sashe