Kankana
Kankana tana daga cikin Tsirrai waɗanda galibin su shuka su akeyi a gonaki musamman farkon Damina da kuma ƙarshen ta. Ana kiranta da fulatanci da (Pariije) A takaice dai Kankana tsiro ce da ake nomawa don amfani da ita kama daga ganyen ta har zuwa ƴaƴanta. Ko kuma Kankana wata abu ce dake ɗauke da wasu ruwa masu zaƙin gaske waɗanda suke da matuƙar amfani ga jikin Ɗan adam. Kankana tana da amfani sosai a jikin bil'adama Ɗan'adam wayanda bazasu lissafu ba daga cikin su akwai ƙarawa mutum ruwan jiki, kariya daga ciwon daji (cancer), kariya daga ciwon zuciya, da kuma kuzari da dai sauransu.[1] Haka kuma ƴaƴan Kankana suma suna matuƙar amfani don ko ba'a barsu a baya ba wajen gina ko amfani a jikin bil'adama. Misali suna ƙara kuzari ga maza, suna kuma maganin ciwon suga (diabetes) da dai sauransu.[2] Haka kuma Kankana tanada amfani sosai a wajen mata masu juna biyu (masu ciki).[3] Kankana Kuma tana ƙara gyara fata da sanya fata gautsi da sheƙi.[4] Kankana tana kuma maganin ciwon ƙoda da kuma ƙara lafiyar idanu (ido).[5] Amfanin Kankana sunada yawa basu lissafuwa, saboda haka take da muhimmanci a rayuwar mu ta yau da kullum.[6][7][8]
Kankana | |
---|---|
dan-ice, abinci, melon (en) da 'ya'yan itace | |
Tarihi | |
Mai tsarawa | Citrullus lanatus var. lanatus (en) da Ruwan Ruwan Ruwa |
.
Amfanin Kankana
gyara sasheKankana na ɗaya daga cikin kayan gona na marmari da ke da matuƙar amfani ga bil'adama. Kankana wata aba ce mai dauke da ruwa mai zaƙi kuma mai amfani matuƙa ga jikin bil'adama. Masana sun bayyana Kankana da ƴa'ƴan ta mai matuƙar amfani ga rayuwar bil'adama, don sindarai da ke cikinta na Vitamins, Minerals, Antioxidants, da kuma Calories. Wasu daga cikin alfanun Kankana goma sha biyu su ne:
- Kankana na dauke da sinadarin dake samar da kariya da rage barazanar cutar hawan jini ga jikin bil'adama (Hypertension)
- Kankana na taimakawa matuka wajen rage yawan kiba da nauyin jiki mai cutar da bil'adama.
- Kankana na dauke da sinadarin “Glutathione” wanda ke taimakawa wajen kwarara garkuwar jikin bil'adama.
- Kankana na dauke da sinadarin “Lycopene” wanda yake dagargaza kwayoyin cutar daji (Cancer)
- Kankana na dauke da sinadarin (Vitamin C) wanda ke da tasiri wajen kashe kwayoyin cutar da ke cikin jinin bil'adama.
- Kankana na dauke da sinadarin “Potassium” wanda ke taimaka wa zuciya, koda, Huhu da sauran muhimman sassan jikin bil'adama.
- Kankana na samar wa fatan bil'adama kariya daga illolin da haske da tsananin zafin rana.
- An bayyana masu shan Kankana da wadanda cutar Asthma za ta yi wuyar kama su saboda sinadarin Vitamin C da Kankana ke da shi (Asthma prevention).
- Kankana na taimaka wa jikin bil'adama wajen narkar da abinci cikin tsari.
- Kankana na samar da kariya da rage barazanar cutar sugar ko Diabetes.
- Kankana na samar da kariya ga cutar ciwon zuciya (Heart Attack).
- Kankana na taimaka wa ma’aurata da kuzari da nishadi musamman a yayin gabatar da ibadan aure.
Hotuna
gyara sashe-
Wani bahaushe kenan da yake ziyara da Kankana
Manazarta
gyara sashe- ↑ Abdulmuminu Sani, Umaymah (15 February 2021). "Sirrin ƴaƴan kankana da ɓawonta ga ma'aurata". BBC Hausa. Retrieved 29 June 2021.
- ↑ Bala Nura, Abubakar (15 May 2018). "Amfanin 'ya'yan kankana 7 a jikin dan adam". legit hausa. Retrieved 29 June 2021.
- ↑ Malumfashi, Muhammad (24 April 2018). "Fa'idar shan kankana ga mata masu dauke da ciki - Masana". legit hausa. Retrieved 29 June 2021.
- ↑ Olusegun, Mustapha (3 February 2017). "Gyaran Fata Da Kankana". aminiya.dailytrust.com. Retrieved 29 June 2021.
- ↑ Aliyu Daudawa, Idris (12 June 2018). "Amfanin Kankana Ga Lafiyar Mutum". leadership Ayau. Retrieved 29 June 2021.
- ↑ Ahmad Janyau, Awwal (11 February 2017). "Amfanin Kankana ga Lafiyar dan Adam". rfi hausa. Retrieved 29 June 2021.
- ↑ "Abubuwa 12 da ake bukatar sha a lokacin tsananin zafi". BBC Hausa. 28 May 2020. Retrieved 29 June 2021.
- ↑ Heritage, Stuart (10 June 2021). "Slice of life: 10 delicious ways to make the most of watermelon". The Guidian. Retrieved 18 September 2021.