Joseph Ogba
Joseph Obinna Ogba (an haife shi a cikin shekarar 1961 a jihar Ebonyi, Najeriya ) ɗan siyasar Najeriya ne. Shi ne Sanata mai wakiltar Ebonyi ta tsakiya a majalisar dattawan Najeriya.[1][2][3] Ɗan majalisar tarayya ne na 8 a Najeriya sannan kuma zaɓaɓɓen ɗan majalisar dattawa a jamhuriya ta 9 ta majalisar dokokin ƙasar.[4][5][6]
Joseph Ogba | |||||
---|---|---|---|---|---|
11 ga Yuni, 2019 - ga Yuni, 2023 District: Ebonyi Central
9 ga Yuni, 2015 - 9 ga Yuni, 2019 ← Joseph Ogba District: Ebonyi Central | |||||
Rayuwa | |||||
Cikakken suna | Joseph Obinna Ogba | ||||
Haihuwa | Ishielu, 1961 (62/63 shekaru) | ||||
ƙasa | Najeriya | ||||
Karatu | |||||
Harsuna |
Turanci Pidgin na Najeriya | ||||
Sana'a | |||||
Sana'a | ɗan siyasa | ||||
Imani | |||||
Jam'iyar siyasa | People's Democracy Party (en) |
Rayuwa ta sirri da ilimi
gyara sasheAn haifi Joseph Ogba a cikin shekarar 1961 a Nkalagu, ƙaramar hukumar Ishielu a jihar Ebonyi, Najeriya. Ya kuma taso ne a Ishielu a takaice. Ogba ya halarci Makarantar Sakandare ta Command da ke Nkalagu inda ya sami shaidar kammala karatunsa a cikin shekarar 1975. Daga nan ya halarci Federal Polytechnic, Oko inda ya samu Diploma da Higher National Diploma a Mass Communication.
Sana'a
gyara sasheOgba ya fara aikinsa ne a matsayin Alƙalin wasa a ƙungiyar alƙalan wasan ƙwallon ƙafa ta Najeriya a cikin shekarar 1986. A shekarar 1995, an naɗa shi Shugaban Hukumar Alƙalan wasan ƙwallon ƙafa ta Najeriya (Anambra State Chapter) kuma ya riƙe muƙamin har zuwa 1997. A cikin shekarar 1997, an naɗa shi memba na Wakilin Gwamnatin Tarayya zuwa Amurka akan Ginin Hoto.
Sana'ar siyasa
gyara sasheA cikin shekarar 1998 ya shiga siyasa aka zaɓe shi shugaban ƙaramar hukumar Ishielu a jihar Ebonyi. Daga nan kuma aka naɗa shi Shugaban Chairmen (ALGON) a Jihar Ebonyi. Saboda ƙwarewarsa a harkar ƙwallon ƙafa, an naɗa shi shugaban ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Ebonyi Angels a cikin shekarar 1999 har zuwa 2002.
Yayin da yake riƙe da muƙamin shugaban ƙungiyar Ebonyi Angels, an naɗa shi kwamishinan matasa da wasanni na jihar Ebonyi a cikin shekarar 2002. A shekarar 2003, bayan ya zama kwamishina aka naɗa shi shugaban hukumar ƙwallon ƙafa ta jihar Ebonyi . A cikin shekarar 2006, ya kasance shugaban kwamitin tallace-tallace da ɗaukar nauyin hukumar ƙwallon ƙafa ta Najeriya.
A lokacin babban zaɓen 2015 a Najeriya, Ogba ya tsaya takarar majalisar dattawa kuma an zaɓe shi a matsayin ɗan majalisar dattawan Ebonyi ta tsakiya.[7] An naɗa shi shugaban kwamitin wasanni a majalisar dattawan Najeriya.[8][9][10] A cikin shekarar 2019, an sake zaɓen shi a majalisar dattawan Najeriya a karo na biyu.[11][12]
Duba kuma
gyara sashe- Jerin mutanen jihar Ebonyi
Manazarta
gyara sashe- ↑ https://www.blueprint.ng/2019-74-candidates-jostle-for-nass-seats-in-ebonyi/
- ↑ https://thenewsnigeria.com.ng/2016/04/05/igbo-group-raises-alarm-over-killing-by-fulani-herdsmen/
- ↑ "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2023-03-19. Retrieved 2023-03-19.
- ↑ https://www.pulse.ng/news/local
- ↑ https://www.vanguardngr.com/2015/09/full-list-of-83-senators-who-passed-vote-of-confidence-on-saraki/
- ↑ "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2023-03-19. Retrieved 2023-03-19.
- ↑ https://nigerianbulletin.com/threads/know-your-senator-see-list-of-nigerias-latest-109-senators.109808/
- ↑ https://www.premiumtimesng.com/news/top-news/192658-saraki-names-senate-committees-heads-rival-ahmed-lawan-gets-defence.html?tztc=1
- ↑ https://www.brila.net/house-representatives-hold-public-hearing-nff-act-next-week/
- ↑ "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2023-03-19. Retrieved 2023-03-19.
- ↑ "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2019-04-05. Retrieved 2023-03-19.
- ↑ https://www.pulse.ng/news/politics/list-of-all-senators-elected-in-2019-national-assembly-elections/nxp70r9