Jami'ar jihar Gombe
Jami'ar Jihar Gombe jami'a ce mallakar gwamnatin jihar Gombe. An kafa ta ne a shekara na 2004.[1] Jami'ar jihar Gombe tana Tudun wada Gombe, Gombe state. Ita member ce ta association of common wealth universities.[2] Shugaban jami'ar wato Chancellor shine sarkin Gombe Alhaji Abubakar Shehu Abubakar II[3] da mataimakinsa wato Vice-Chancellor Professor Aliyu Usman Elnafaty[4]. Farkon maitamakin shugaba na jami'ar (Vice Chancellor) shine farfesa Abdullahi Mahadi[5].
Jami'ar jihar Gombe | |
---|---|
| |
Primus Inter Pares(first among equals) | |
Bayanai | |
Iri | jami'a |
Ƙasa | Najeriya |
Aiki | |
Mamba na | Ƙungiyar Jami'in Afrika da Association of Commonwealth Universities (en) |
Babban mai gudanarwa | Aliyu Usman El-Nafaty |
Tarihi | |
Ƙirƙira | 2004 |
|
Governor Muhammad Danjuma Goje ne ya kafa jami'ar a shekaran 2004.
Jami'ar jihar Gombe an samar da ita a shekarar 2003 karkashin mulkin gwamna Muhammad Danjuma Goje. Hukumar ilimi ta jihar Gombe ta samar da shuwagabanni da manazarta na jami'ar kimanin mutane ashirin da hudu 24 wanda zasu kula da harkokin ilimi na jami'ar. Jami'ar tana samarda dalibai da suka kammala karatun gaba da sakandare a fannoni daban daban
Shuwagabannin Jami'ar
gyara sasheMarigayi Farfesa Abdullahi Mahadi shi ne shugaban jami'ar na farko. Kafin shiga Jami’ar Jihar Gombe a matsayin shugaban jami’ar a lokacin da aka kafa jami’ar a shekarar 2004, Mahdi ya yi aiki irin nasa a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya na tsawon shekaru hudu. Ya kasance Shugaban Jami’ar Jihar Gombe tun daga shekarar 2005 zuwa 2014, lokacin da Gwamnan Jihar Gombe na lokacin Ibrahim Hassan Dankwambo[6] ya naɗa Farfesa Ibrahim Umar a matsayin Shugaban Jami’ar.[7]
Kafin nadin nasa Farfesa Ibrahim Umar shi ne shugaban tsangayar kimiyya da karatun digiri na biyu na jami'ar. An haife shi a shekarar alif ɗari tara da hamsin da takwas (1958) a karamar hukumar Nafada,[8] dake Jihar Gombe.
Shugaban jami'ar na yanzu shine Farfesa Aliyu Usman El-Nafaty a matsayin shugaban jami'ar jihar Gombe na uku bayan karewar wa'adin Prof. I. M Umar a shekarar 2019.[9][10][11][12][13]
Sashuna
gyara sasheSashuna da ke ƙarƙashin Jami’ar Jihar Gombe:[14]
Sashen Arts da Social Sciences[20]
gyara sashe- Accounting
- Business Administration
- Economics
- English Language
- History
- Political Science
- Public Administration
- Religious
- Sociology
Sashen Ilimi
gyara sasheWannan sashe ya ƙunshi manyan sassa guda uku (3)[21], wanda ko wani sashe daga cikin su yana da rassa a ƙarƙashin sa. Sashunan sune kamar haka;
- Sashen Arts and Social Sciences Education
- Sashen Educational Foundation
- Sashen Science Education
Sashen kimiyya[22]
gyara sashe- Biological Sciences
- Biochemistry
- Botany
- Chemistry
- Computer Science
- Geography
- Geology
- Mathematics
- Microbiology
- Physics
- Science Laboratory Technology
- Zoology
Sashen Pharmaceutical Science[23]
gyara sashe- Pharmacognosy and Drug Development
- Pharmaceutics and Pharmaceutical Technology
- Clinical Pharmacy and Pharmacy Practice
- Pharmaceutics and Medicinal Chemistry
- Pharmacology and Therapeutics
- Pharmaceutical Microbiology
Kwalejin Kimiyyar Lafiya[24]
gyara sasheKwalejin kimiyyar likitanci ta ƙunshi sassa uku;
- Sashen Medical Sciences
- Sashen Basic Clinical Sciences
- Sashen Clinical Sciences
Makarantar Digiri na gaba
gyara sasheAn kafa Makarantar Digiri na biyu ne ta hanyar sashe na 7 (i) a na Dokar Jami’ar Jihar Gombe ta 2004. Yayin da aka fara aiwatar da shirin a shekarar 2008/2009, an bude Makarantar Koyon Digiri na farko a ranar 30 ga Yuli, 2009. Duk da haka, darussa uku ne aka fara daga 2012/2013, wato: MA History, M.Sc. Physics da PGDE. Biyo bayan haɓaka da aka samu a cikin 2014/2015, Makarantar Digiri na biyu a halin yanzu tana gudanar da darussa sittin da takwas a ƙarƙashin sashunan karatu uku.[25][26]
Dakin Karatu
gyara sasheAkwai babban ɗakin karatu guda ɗaya a cikin jami'ar.
Babban dakin karatu na jami'ar wani gini ne mai hawa biyu wanda ke cikin babban jami'ar mai dauke da ofisoshi daban-daban, sassan da ke dauke da ma'aikatan gudanarwa, fasaha da sauran ma'aikata. Dakin karatun yana da tarin litattafai masu tarin yawa fiye da 52,000 da lakabi na lokaci-lokaci 12,000, da kuma fa'idodin mujallolin kan layi da na layi. Dakin karatun yanada sashi na musamman na yanar gizo (online) inda akwai na'urai na konfuta da dama domin dalibai masu aikin bincike (wato research da project} [27]Yanzu kuma an sanya wa dakin karatu sunan marigayi Farfesa Abdullahi Mahdi, wanda ya kasance tsohon shugaban jami’ar kuma shugaban jami’ar na farko[28].
Hotuna
gyara sashe
Manazarta
gyara sashe- ↑ "Gombe State University". www.4icu.org. Retrieved 16 March 2019.
- ↑ ^ "Gombe State University" . www.4icu.org. Retrieved 9 March 2013.
- ↑ Abubakar Shehu-Abubakar - Wikipedia
- ↑ The Vice Chancellor – Gombe State University (gsu.edu.ng)
- ↑ Abdullahi Mahadi - Wikipedia
- ↑ https://dailytrust.com/dankwambo-how-ex-gov-who-forgot-he-had-left-power-missed-his-flight-seeking-vip-treatment/
- ↑ https://www.premiumtimesng.com/regional/nnorth-east/168363-dankwambo-appoints-new-gombe-state-university-v-c.html?tztc=1
- ↑ https://gsu.edu.ng/home/the-vice-chancellor/
- ↑ https://www.premiumtimesng.com/regional/nnorth-east/168363-dankwambo-appoints-new-gombe-state-university-v-c.html
- ↑ https://tribuneonlineng.com/tetfund-pillar-of-development-in-gombe-state-university-%E2%80%94-vc/[permanent dead link]
- ↑ https://blerf.org/index.php/biography/umar-professor-ibrahim-musa/
- ↑ https://dailytrust.com/prof-mahdi-appointed-vc-gombe-tech-varsity
- ↑ https://gsu.edu.ng/home/the-vice-chancellor/
- ↑ 14.0 14.1 https://gsu.edu.ng/home/about-us/
- ↑ Faculties – Gombe State University (gsu.edu.ng)
- ↑ Faculties – Gombe State University (gsu.edu.ng)
- ↑ Faculties – Gombe State University (gsu.edu.ng)
- ↑ Faculties – Gombe State University (gsu.edu.ng)
- ↑ Faculties – Gombe State University (gsu.edu.ng)
- ↑ List of FOASS – Gombe State University (gsu.edu.ng)
- ↑ https://gsu.edu.ng/home/dean-of-education/
- ↑ Faculty of Science – Gombe State University (gsu.edu.ng)
- ↑ Faculties – Gombe State University (gsu.edu.ng)
- ↑ Faculties – Gombe State University (gsu.edu.ng)
- ↑ https://gsu.edu.ng/home/
- ↑ https://www.eafinder.com/ng/list-of-postgraduate-courses-offered-at-gombe-state-university-gsu/,%20https://www.eafinder.com/ng/list-of-postgraduate-courses-offered-at-gombe-state-university-gsu/[permanent dead link]
- ↑ University Librarian – Gombe State University (gsu.edu.ng)
- ↑ University Librarian – Gombe State University (gsu.edu.ng)