James O. C. Ezeilo
James Okoye Chukuka Ezeilo (17 Janairu 1930 - 2013) shi ne farfesa na farko a fannin lissafi a Najeriya. Sau da yawa ana yi masa kallon uban lissafin zamani a kasar[1] kuma shi ne shugaban Jami'ar Najeriya, Nsukka na biyar. Ya kasance shugaban Jami'ar Bayero Kano daga 1977 zuwa 1978. Ya kasance tsohon dalibin Jami'ar Cambridge kuma ya rasu a shekara ta 2013.[2]
James O. C. Ezeilo | |
---|---|
Rayuwa | |
Cikakken suna | James Okoye Chukuka Ezeilo |
Haihuwa | Nanka (en) , 17 ga Janairu, 1930 |
ƙasa | Najeriya |
Harshen uwa | Harshen, Ibo |
Mutuwa | Lagos,, 4 ga Janairu, 2013 |
Karatu | |
Makaranta |
Jami'ar Ibadan (1949 - 1955) University of Cambridge (en) (1955 - 1959) |
Thesis | ' |
Thesis director | Mary Cartwright (mul) |
Dalibin daktanci |
Haroon Tejumola (en) Anthony Nnemeka Eke (en) |
Harsuna |
Turanci Harshen, Ibo Pidgin na Najeriya |
Sana'a | |
Sana'a | masanin lissafi |
Employers |
Jami'ar Ibadan (1959 - 1963) University of Michigan (en) (1963 - 1964) Jami'ar Ibadan (1964 - 1966) Jami'ar Najeriya, Nsukka (1966 - 1978) Jami'ar Bayero (1978 - 1979) Howard University (en) (1979 - 1980) Jami'ar Najeriya, Nsukka (1980 - 1988) Jami'ar Botswana (1997 - 1998) University of Eswatini (en) (1998 - 2001) Ebonyi State University (2002 - 2009) |
Kyaututtuka |
gani
|
Mamba |
The World Academy of Sciences (en) Makarantar Kimiyya ta Najeriya |
Ya fara yin amfani da mahawara nau'in digiri na Leray-Schauder don samun sakamako na wanzuwa don warware matsalolin yau da kullun na daidaitattun daidaito.[3]
Girmamawa
gyara sasheKasancewan shi daya daga cikin tsoffin shugabannin Jami’ar Bayero Kano, an sanya wa wani gidan wasan kwaikwayo mai suna J. O. C. Ezeilo Twin theatre wanda ke tsohon harabar Jami'ar Bayero daura da sashen nazarin ilimin halittar dan Adam.
Manazarta
gyara sashe- ↑ "James O. C. Ezeilo". Mathematicians of the African Diaspora. The Mathematics Department of The State University of New York at Buffalo. Retrieved 20 December 2017.
- ↑ "Professor James O. C. Ezeilo". Edward Bouchet Abdus Salam Institute. Retrieved 20 December 2017.
- "J.O.C. Ezeilo (1930–2013)". The Sun News (Nigeria). EBASI. Retrieved 20 December 2017. - ↑ "James O. C. Ezeilo". Mathematicians of the African Diaspora. The Mathematics Department of The State University of New York at Buffalo. Retrieved 21 January 2018.