Issaku Salia
Issahaku Salia ɗan siyasar Ghana ne kuma mai gudanarwa. Ya taɓa zama ɗan majalisa mai wakiltar mazabar Wa ta Gabas a Upper West daga ranar 7 ga watan Janairun 1993 zuwa 6 ga watan Janairun 2005. Ya kuma taɓa zama ministan yankin Upper West.[1][2][3]
Issaku Salia | |||||
---|---|---|---|---|---|
7 ga Janairu, 2001 - 6 ga Janairu, 2005 District: Wa East Constituency (en) Election: 2000 Ghanaian general election (en)
7 ga Janairu, 1997 - 6 ga Janairu, 2001 District: Wa East Constituency (en) Election: 1996 Ghanaian general election (en) | |||||
Rayuwa | |||||
Haihuwa | 15 ga Yuni, 1952 (72 shekaru) | ||||
ƙasa | Ghana | ||||
Karatu | |||||
Makaranta | University of Ghana Digiri a kimiyya : Kimiyyar siyasa | ||||
Harsuna | Turanci | ||||
Sana'a | |||||
Sana'a | ɗan siyasa da administrator (en) | ||||
Imani | |||||
Addini | Musulunci |
Rayuwar farko da ilimi
gyara sasheAn haifi Issahaku Salia a ranar 15 ga watan Yunin 1952 a garin Manwe dake yankin Upper West na kasar Ghana. Ya halarci Jami'ar Green Hill (a yanzu Ghana Institute of Management and Public Administration (GIMPA)), inda ya sami Difloma a fannin Gudanar da Jama'a, a Jami'ar Ghana inda ya sami digiri na farko a Kimiyyar Siyasa. Salia yana raye. [4]
Siyasa
gyara sasheYa kasance memba na majalisar dokoki ta 1, 2 da ta 3 na jamhuriya ta 4 ta Ghana.[5]
Zaɓen 1992
gyara sasheAn fara zaɓen shi a matsayin ɗan majalisa a kan tikitin jam'iyyar National Democratic Congress don wakiltar mazaɓar Wa ta Gabas a yankin Upper West na Ghana a lokacin zaɓen 'yan majalisar dokokin Ghana na 1992. Ya fara aiki a matsayin memba na majalisar farko ta jamhuriya ta huɗu ta Ghana a ranar 7 ga watan Janairun 1993.
Zaɓen 1996
gyara sasheYa zama ɗan majalisa ta 2 a ranar 7 ga watan Janairun 1997 bayan da aka ayyana shi a matsayin wanda ya lashe babban zaɓen ƙasar Ghana na 1996 bayan ya doke Boyela Insah na sabuwar jam'iyyar Patriotic Party. Ya samu kashi 56.70% na kuri'un da aka kaɗa wanda yayi daidai da kuri'u 22,078 yayin da 'yan adawar sa suka samu kashi 16.60% wanda yayi daidai da kuri'u 6,445.[6]
Zaɓen 2000
gyara sasheAn zaɓe shi a matsayin ɗan majalisa na tikitin jam'iyyar National Democratic Congress a lokacin babban zaɓen Ghana na shekarar 2000 mai wakiltar mazaɓar Wa ta Gabas a yankin Upper West na Ghana.
Ya samu kuri'u 14,278 daga cikin kuri'u 25,795 da aka kaɗa wanda ke wakiltar kashi 55.40%[7] Bayon Godfrey Tangu, sabon ɗan jam'iyyar Patriotic Party ne ya doke shi a lokacin babban zaɓen shekara ta 2004.[8]
Mataimakin shugaban ƙasa ne ya gabatar da shi a ranar 1 ga watan Agusta, 2010 ga sarakuna da al'ummar yankin a matsayin ministan yankin Upper West.
Sana'a
gyara sasheSalia tsohon ɗan majalisa ne mai wakiltar mazaɓar Wa ta Gabas a yankin Upper West na Ghana. Shi ma administrator ne. [4]
Rayuwa ta sirri
gyara sasheManazarta
gyara sashe- ↑ "Veep introduces Alhaji Salia as Upper West Minister". www.ghanaweb.com (in Turanci). 2010-08-01. Retrieved 2020-09-04.
- ↑ "Journalists urge politicians to respect time". MyJoyOnline.com (in Turanci). 2011-07-20. Retrieved 2020-09-04.
- ↑ admin. "admin – Page 8 – MLGR" (in Turanci). Archived from the original on 2021-10-21. Retrieved 2020-09-04.
- ↑ 4.0 4.1 4.2 Ghana Parliamentary Register(2004-2008)
- ↑ Ghana Parliamentary Register 1992-1996. Ghana Publishing Corporation. 1993. p. 345.
- ↑ FM, Peace. "Ghana Election 1996 Results - Wa East Constituency". Ghana Elections - Peace FM. Retrieved 2020-10-17.
- ↑ Peace FM. "Parliament - Wa East Constituency Election 2000 Results". Ghana Elections - Peace FM. Retrieved 2020-09-04.
- ↑ Peace FM. "Ghana Election 2004 Results - Wa East Constituency". Ghana Elections - Peace FM. Retrieved 2020-09-04.