Ibrahim Yahaya Oloriegbe
Ibrahim Yahaya Oloriegbe babban likitan Najeriya ne, dan siyasa kuma mai taimakon jama’a. Oloriegbe ya kammala karatun digiri na MBBS daga Jami'ar Ahmadu Bello, Zariya, Nijeriya a shekarar alif ta.1985. Ya halarci shirye-shiryen horarwa akan Gudanar da Canji, Ba da Shawarwari, Karfafawa, Gudanar da Ayyuka, manufofin kiwon lafiya da nazarin tsarin, Dokoki, Shugabanci da Tsarin Gudanarwa kan Koyawa da Tattaunawa kan Canji a Jami'ar Oxford ta Burtaniya.
Ibrahim Yahaya Oloriegbe | |||
---|---|---|---|
ga Yuni, 2019 - District: Kwara central | |||
Rayuwa | |||
Cikakken suna | Ibrahim Yahaya Oloriegbe | ||
Haihuwa | Kwara, | ||
ƙasa | Najeriya | ||
Karatu | |||
Harsuna |
Turanci Pidgin na Najeriya | ||
Sana'a | |||
Sana'a | ɗan siyasa | ||
Imani | |||
Jam'iyar siyasa | All Progressives Congress |
A matsayinsa na dan siyasa, ya kasance shugaban masu rinjaye a Majalisar Dokoki na Jihar Kwara tsakanin shekara ta 1999 zuwa 2003.[1] Ya tsaya takara a zaben shekara ta 2011, inda ya sha kayi daga hannun Sen. Bukola Saraki. A shekara ta 2019, ya kuma tsaya takarar kujerar dan majalisar dattawa mai wakiltar Kwara ta Tsakiya wanda ya kayar da shugaban majalisar dattijan Najeriya mai ci Sen. Bukola Saraki.[2]
Kuruciya, Ilimi da Aiki
gyara sasheAn haifi Oloriegbe a ranar 12 ga watan Nuwamban shekara ta 1960. Ya kammala karatunsa daga Jami'ar Ahmadu Bello, Zariya a shekara ta 1985 tare da Digirin farko a likitanci, Digirin tiyata na Digiri (MB. BS). Yana da ƙololuwar sakamako a fannukan kimiyyar halittar dan adam, Biochemistry, Magungunan Jama'a da Magungunan dakunan gwaje-gwaje. Ya sami ƙarin horo a kan nazarin Tsarin Kiwan lafiya, Gudanar da Canji (Consulting and Coaching for Change) da Gudanar da Ayyukan Kiwon lafiya. Ya kammala digiri na biyu a Kimiyya a fannin Tuntuba da Koyarwa don Canji, (Babban Shirin Gudanarwa wanda Jami'ar Oxford, UK da HEC Business School, Paris ke gudanarwa) a watan Oktoban shekara ta 2006. Oloriegbe ya yi aiki a matsayin likita a fannin Kiwon Lafiya na Nijeriya tun daga shekara ta 1985. Ya yi aiki a bangarorin gwamnati da na 'yan kasuwa. Ya kasance Daraktan lafiya na asibitin Al-barka da ke Kano da kuma Oloriegbe Clinic & Maternity Hospital, Ilorin da dai sauransu. Ya kasance shugaba a Kungiyar Likitocin Najeriya (NMA), Kungiyar Likitocin Gwamnati da na 'Yan Kasuwa na Nijeriya (AGPMPN) da kuma Guild of Medical Directors (GMD). Ya kasance Sakatare Janar na NMA a Kano daga shekara ta (1991 zuwa 1994), a lokacin ya kasance memba na Majalisar Zartarwa ta Kasa ta NMA. Ya kuma kasance Sakataren AGPMPN da GMD na Kano a tsakanin shekarun 1992 zuwa 1994.
Iyali
gyara sasheOloriegbe ya yi aure yana da 'ya'ya 4.[3]
Harkar siyasa
gyara sasheOloriegbe ya tsaya takara kuma an zabe shi matsayin dan majalisar dokokin Kwara a karkashin jam'iyyar All Nigeria Peoples Party (ANPP). Ya kuma kasance shugaban masu rinjaye, Shugaban Kwamitin Majalisar kan Lafiya da Kwamitin Gida a Kananan Hukumomi daga shekara ta 1999-2003. Ya kasance memba na Action Congress of Nigeria (ACN) sannan kuma ya tsaya takarar sanata na mazabar Kwara ta tsakiya a karkashin jam’iyyar tare da Bukola Saraki a shekara ta 2011 wato Gwamnan Jihar Kwara na lokacin.
A zaben ranar 23 ga watan Fabrairun, shekara ta 2019 na zaben sanata mai wakiltar yankin Kwara ta Tsakiya, an zabe shi a matsayin Sanata mai wakiltar yankin Kwara ta Tsakiya inda ya kayar da Bukola Saraki gwamna mai ci.[4][3] A shekara ta 2022, Oloriegbe ya rasa neman kujerar sanata mai wakiltar Kwara ta Tsakiya a zaben fidda gwani na jam'iyyar APC ga Saliu Mustapha.[5]
Awards and Honours
gyara sashe- HONORARY CITIZEN, GEORGIA STATE, U.S.A- 2003 [6]
- BEST STUDENT PRICES IN PHYSICS, CHEMISTRY, BIOLOGY MATHEMATICS, ECONOMICS AND GEOGRAPHY IN A.I.S.S ILORIN-1979[7]
Kyaututtuka da Girmamawa
gyara sasheManazarta
gyara sashe- ↑ https://www.pmnewsnigeria.com/2019/02/24/apc-senatorial-candidate-oloriegbe-overthrows-saraki-in-kwara/
- ↑ "Oloriegbe: Universal participation in elections allows better representation". The Guardian Nigeria News - Nigeria and World News. 2020-08-23. Retrieved 2022-02-21.
- ↑ 3.0 3.1 "Meet Oloriegbe".
- ↑ "End of road for Saraki as Oloriegbe wins". guardian.ng. The Guardian. Archived from the original on 26 February 2019. Retrieved 13 March 2019.
- ↑ "Kwara Central senator loses ticket, Mustapha, Ashiru, Sodiq win". Vanguard Nigeria. Demola Akinyemi.
- ↑ https://www.nassnig.org/mps/single/24
- ↑ https://www.nassnig.org/mps/single/24
- ↑ https://www.nassnig.org/mps/single/24
- ↑ https://www.nassnig.org/mps/single/24