Haruna Manu
Haruna Manu (an haife shi ranar 23 Ga watan Augusta shekarar 1973) dan siyasa ne a Najeriaya kuma mamba na jamiyyar PDP sannan kuma tsohon mamba a majalisar wakilai ta tattauna, ya wakilai Bali/Gassol Federal Constituency. Shine mataimakin gwamnan Jihar Taraba, yana mataimakin ne karkashin gwamna Darius Dickson Ishaku tun daga 29 ga watan Mayu, shekarar 2015.[1][2][3][4]
Haruna Manu | |||||
---|---|---|---|---|---|
13 ga Yuni, 2023 - ← Yusuf Abubakar Yusuf District: Taraba Central
29 Mayu 2015 - 29 Mayu 2023 | |||||
Rayuwa | |||||
Haihuwa | 23 ga Augusta, 1973 (51 shekaru) | ||||
ƙasa | Najeriya | ||||
Mazauni | Jalingo | ||||
Sana'a | |||||
Sana'a | ɗan siyasa da injiniya | ||||
Imani | |||||
Jam'iyar siyasa | People's Democratic Party (en) |
Rayuwa da Ilimi
gyara sasheAn haifi Haruna a ranar 23 ga watan Agusta, shakarar 1973, a wani gari da ake kira da Mutum-Biyu, a karamar hukumar Gassol ta jihar Taraba. Ya yi digiri na farko a fannin harkokin kasuwanci (Business Administration) tare da samun kwarewa a fannin hada-hadar kudi daga babbar Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zariya a jihar Kaduna. Ya kuma yi digirin digirgir a fannin Kasuwancin Lantarki daga Jami’ar Carnegie Mellon da ke Amurka, kuma ya samu sheda a certified Microsoft System Engineer.
Aiki
gyara sasheYayi aiki da Nigerian Liquefied Natural Gas (NLNG) ya kuma yi aiki a kamfanin sadarwa na Nigeria Communication Limited (MTN) a takaice yayi aiki a kamfanoni dama.
Manazarta
gyara sashe- ↑ "Taraba seeks Senate intervention over N30b spent on FG roads". The Guardian Nigeria News - Nigeria and World News (in Turanci). 2017-11-15. Archived from the original on 2022-02-22. Retrieved 2022-02-22.
- ↑ "Looters will be arrested, says Taraba deputy gov". Punch Newspapers (in Turanci). 2020-10-26. Retrieved 2022-03-12.
- ↑ "Office of the Deputy Governor". tarabastate.gov.ng. Archived from the original on October 8, 2020. Retrieved November 10, 2020.
- ↑ "Inec Declares Darius Ishaku winner of Taraba Governorship Election". Channels TV. April 26, 2015. Retrieved November 10, 2020.