Yusuf Abubakar Yusuf
Yusuf Abubakar Yusuf (an haife shi a ranar 5 ga watan Nuwamba na shekara ta 1956) ɗan siyasan Najeriya ne wanda ya kasance ɗan majalisar dattawa a ƙarƙashin jam'iyyar APC mai mulki, yana wakiltar mazaɓar Taraba ta tsakiya tun shekara ta 2015.[1][2] An bayyana shi a matsayin wanda ya lashe kujerar majalisar dattawa a ranar 26 ga watan Nuwamba shekarata 2015 bayan kotun zaɓe ta tabbatar dashi, sai kuma kotun ɗaukaka ƙara ta bayyana haka bayan babban zaɓen Najeriya nashekanasheka 2015. A baya dai an bayyana ɗan takarar jam’iyyar na PDP Bashir Marafa a matsayin wanda ya lashe zaɓen, amma Yusuf Abubakar Yusuf ya maye gurbinsa bayan da kotun ta gano akwai kura-kurai a zaɓen.[3][4]
Yusuf Abubakar Yusuf | |||||
---|---|---|---|---|---|
9 ga Yuni, 2015 - District: Taraba Central
District: Taraba Central | |||||
Rayuwa | |||||
Haihuwa | Nguroje (en) , 2 Disamba 1956 (68 shekaru) | ||||
ƙasa | Najeriya | ||||
Karatu | |||||
Makaranta | Jami'ar Ahmadu Bello | ||||
Sana'a | |||||
Sana'a | ɗan siyasa | ||||
Employers | Jami'ar Maiduguri | ||||
Imani | |||||
Jam'iyar siyasa | All Progressives Congress |
Rayuwar Farko da Ilimi
gyara sasheAn haife shi a Nguroje, ya yi karatu a Jami’ar Ahmadu Bello inda ya samu digirn farko wato (BSc Economics, 1980) haka kuma yayi karatun digirin-digirgir a Jami’ar East Anglia (MA Economics, 1983). Haka kuma mamba ne a wata kungiya ta tsangayar karatu a jami'ar Maiduguri.[5]
Manazarta
gyara sashe- ↑ "N5bn monthly not enough for 2.7m IDPs – Senator" (in Turanci). 2020-09-07. Retrieved 2022-02-21.
- ↑ "Taraba tribunal sacks Senator Marafa". The Nation (Nigeria). Retrieved 27 March 2016.
- ↑ "Tribunal sacks PDP senator in Taraba". National Mirror. Archived from the original on March 27, 2016. Retrieved 27 March 2016.CS1 maint: unfit url (link)
- ↑ "Tribunal declares APC candidate winner of Taraba Central senatorial election". Vanguard (Nigeria). Retrieved 27 March 2016.
- ↑ "Sen. Yusuf Abubakar Yusuf". National Assembly (Nigeria). Retrieved 27 March 2016.