Harin bom a Potiskum, 2014
A watan Nuwamba ta shekara r dubu biyu da goma Sha hudu 2014, an kai wasu hare-haren ta'addanci sau biyu a garin Potiskum da ke jihar Yobe a Najeriya. Dukkan Hara-haren kwara biyu sun hada da; harin ƴan ƙuna baƙin wake, inda suka kashe aƙalla mutane 61 tare da jikkata wasu da dama. Ana dai zargin kungiyar Boko Haram a matsayin wadda ta kai hare-haren.
Harin bom a Potiskum | ||||
---|---|---|---|---|
suicide bombing (en) | ||||
Bayanai | ||||
Bangare na | Rikicin Boko Haram | |||
Ƙasa | Najeriya | |||
Kwanan wata | 10 Nuwamba, 2014 | |||
Wuri | ||||
|
Kai hari
gyara sasheA kan ƴan Shi'a
gyara sasheA ranar 3 ga watan Nuwamban shekarar 2014, wani ɗan ƙuna baƙin wake ya kashe aƙalla mutane 15 a wani hari da aka kai wa ƴan shi'a, a lokacin da suke tsaka da gudanar da tattakin tunawa da ranar Ashura. Kimanin mutane 50 ne suka jikkata a harin, yayin da jami’an tsaro suka harbe wasu biyar.[1][2][3]
A makarantar gwamnati
gyara sasheA ranar 10 ga watan Nuwamba, 2014, kusan adadin mutane 46 ne suka mutu sannan 79 suka jikkata a wani harin kuma na ƙuna baƙin wake da aka kai a Potiskum, jihar Yobe, Najeriya. An kai harin ne a lokacin da dalibai suka taru a ɗakin taro na Makarantar Sakandaren Kimiyya ta Gwamnati. Maharin ya shiga makarantar sanye da kayan makaranta a matsayin basaja. Bayan harin, gwamnan jihar ya rufe dukkan makarantun gwamnati a yankin.[4][5]
Duba kuma
gyara sasheManazarta
gyara sashe- ↑ "Nigeria Shias in Potiskum hit by 'suicide attack'". BBC News. Retrieved 10 November 2014.
- ↑ "Suicide blast kills 29 in Nigeria, prison attack frees 144". Reuters. Retrieved 10 November 2014.
- ↑ AFP. "Blast hits Shia ceremony in Nigeria's Yobe". Retrieved 10 November 2014.
- ↑ "Suicide bomber kills 48 students in Nigeria". Yahoo News. 10 November 2014. Retrieved 10 November 2014.
- ↑ "Nigeria school blast 'kills 47 students' in Potiskum". BBC. 10 November 2014. Retrieved 10 November 2014.