Hari a Ginin Majalisar Dinkin Duniya dake Abuja, 2011
Harin da aka kai a Abuja a shekara ta 2011 wani harin bam ne da aka dasa a cikin mota a ranar Juma’a, 26 ga watan Agusta, 2011 a ginin Majalisar Ɗinkin Duniya da ke Abuja babban birnin Najeriya, wanda ya kashe aƙalla mutane 21 tare da raunata wasu su 60. Daga baya mai magana da yawun ƙungiyar ƴan Boko Haram ya ɗauki alhakin kai harin.[1]
| ||||
Iri |
suicide car bombing (en) aukuwa | |||
---|---|---|---|---|
Kwanan watan | 26 ga Augusta, 2011 | |||
Wuri | Abuja | |||
Adadin waɗanda suka rasu | 23 | |||
Adadin waɗanda suka samu raunuka | 73 |
Da misalin ƙarfe 11:00 na safe a yankin diflomasiyya da ke tsakkiyar birnin, wata mota ɗauke da bam ta kutsa cikin shingen tsaro guda biyu. Daga nan direban motar ya tayar da bam ɗin bayan ya kitso da motar a cikin ɗakin karɓar baki na Majalisar Dinkin Duniya. Bam din ya yi ɓarna a benayen ginin. An ce hedkwatar ma'aikatan Majalisar Dinkin Duniya kusan ma'aikata 400 ne, amman ba a san adadin mutanen da ke cikin ginin ba, a lokacin da aka kai harin.
Wani reshe na ginin ya ruguje kuma kasan ginin, ginin ya lalace sosai. Jami’an bayar da agajin gaggawa sun yi gaggawar kwashe gawarwakin ginin tare da garzayawa da waɗanda suka jikkata zuwa asibiti. An kawo injin ɗaga kaya-(cranes) zuwa wurin da fashewar ta auku domin kwashe ɓara-guzan gine-gine wurin, da kuma tabbatar da cewa babu wanda ya maƙale a wurin.[2]
Fashewar ta yi sanadiyar mutuwar aƙalla mutane 21 tare da jikkata 73. Karamar Ministar Harkokin Waje, Viola Onwuliri ta ce: "Wannan ba hari ba ne ga Najeriya amma ga al'ummar duniya. An kai hari a duniya."[2] Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon ya bayyana harin a matsayin 'kai hari kan waɗanda suka sadaukar da kansu wajen taimakon wasu'[3] Harin shi ne harin kunar bakin wake na farko a Najeriya da aka kai wa wata ƙungiya ta ƙasa da ƙasa hari.[4]
A watan Satumban 2011 Hukumar Tsaron Ma’aikatar Harkokin Wajen Najeriya ta yi zargin cewa Mamman Nur ne ya shirya harin inda ta bayar da ladar Naira miliyan 26 (US $160,000).[5][6] Haka kuma wasu mutane huɗu sun bayyana a wata kotun majistare da ke Abuja da ake zargi su, da shirya harin bam, kuma an tura su gidan yari zuwa wata babbar kotun tarayya.
Duba kuma
gyara sasheManazarta
gyara sashe- ↑ Nossiter, Adam (28 August 2011). "Islamic Group Says It Was Behind Fatal Nigeria Attack". The New York Times. Retrieved 28 August 2011.
- ↑ 2.0 2.1 BBC (26 August 2011). "Abuja attack: Car bomb hits Nigeria UN building". BBC News. Retrieved 26 August 2011.
- ↑ "Abuja bombing: UN offices hit by deadly blast". The Guardian. Retrieved on 28 August 2011.
- ↑ "Terrorism in Nigeria: A dangerous new level". The Economist. 3 September 2011. Retrieved 7 September 2011.
- ↑ "Nigerian authorities seek alleged mastermind of deadly UN headquarters bombing". The Washington Post. 18 September 2011.[dead link]
- ↑ Imobo-Tswam, Simon (19 September 2011). "Nigeria: UN Building – Video of Boko Haram Bomber Released". allAfrica.com. Missing or empty
|url=
(help)
9°03′00″N 7°30′00″E / 9.0500°N 7.5000°E9°03′00″N 7°30′00″E / 9.0500°N 7.5000°E