Hari a Chakawa da Kawu

Kisan kiyashin da ya faru a watan Janairun 2014

Hare-haren Arewacin Najeriya a watan Janairun 2014 wani jerin kisan kiyashi ne na ƴan ta’adda da suka faru a watan Janairun shekara ta dubu biyu da goma Sha hudu 2014 a Kawuri, Jihar Borno da kuma a kauyen Chakawa, karamar Hukumar Madagali, Jihar Adamawa (hari a lokaci ɗaya, amman wuri daban-daban). An dai ɗora alhakin dukkan hare-haren kan ƴan kungiyar Boko Haram wacce tayi ƙaurin suna wajen kai hare-hare, musamman a yankin arewa maso gabashin Najeriya.

Kadan daga cikin yan bindigan dake kai hare hare
Infotaula d'esdevenimentHari a Chakawa da Kawu
Iri Kisan Kiyashi
Kwanan watan ga Janairu, 2014
Ƙasa Najeriya
Adadin waɗanda suka rasu 138

A ranar 31 ga watan Janairu, an kashe wani fasto da membobin ikilisiyarsa su 10 a Chakawa. [1] [2]

26 ga watan Janairu

gyara sashe

A daren ranar ashirin da shida 26 ga watan Janairu an kai wasu hare-hare guda biyu a Kawuri, jihar Borno da cocin Katolika ta ƙauyen Chakawa, karamar hukumar Madagali, jihar Adamawa . [3] [4] [5]

A Kawuri, wani ƙauye a karamar hukumar Konduga, jihar Borno (wanda ke da tazarar kilomita 37 daga kudu maso gabashin Maiduguri ), an kashe mutane 85 cikin dare. [6] [7] [8] Ana dai ɗora alhakin hare-haren kan kungiyar Boko Haram . [9]

A Chakawa (garin da aka fi sani da sunan Waga Chakawa) an yanka maƙogwaron wasu da yawa daga cikin masu bauta a cocin,[10] yayin da aka harbe wasu. An kiyasta cewa an kashe mutane 31, [11] amma adadin ya ƙari zuwa 41. [12]

Adadin waɗanda suka mutu na karshe ya kai a ƙalla jummullar mutane 138. [13]

Manazarta

gyara sashe
  1. Gunmen invade church, kill pastor, 10 worshippers in Adamawa. Samuel Agada, Daily Post Nigeria. February 2, 2014.
  2. Kill Pastor, 10 worshippers In Adamawa. February 2, 2014 - 5:31am | Lara Adejoro, Daily Times of Nigeria.
  3. BBC world news, 27 January 2014.Nigeria 'Boko Haram' attacks leave scores dead.
  4. Communal unrest turns deadly in Nigeria. AlJazeera English website. Accessed 25 May 2014.
  5. Gunmen kill worshippers at Nigeria church. AlJazeera English website. Accessed 25 May 2014.
  6. HARUNA UMAR. 85 dead in Nigerian village massacre. January 28, 2014 at 09:14pm.
  7. Boko haram: 85 dead and counting in northeast Nigeria village Archived 2014-05-29 at the Wayback Machine, Wednesday, 29 January 2014 12:36.
  8. Reuters News Agency.Death toll in northeast Nigeria attack rises to 85 Archived 2020-07-28 at the Wayback Machine, Tue Jan 28, 2014.
  9. Ibrahim-Gwamna Mshelizza. Not Less Than 50 Killed In Kawuri Today. The Nigerian Voice. 27 January 2014.
  10. "How Boko Haram Slit Throats Of Church Worshippers In Adamawa [GRAPHIC] | 9JAOLOFOFO™". 9jaolofofo.com.ng. Archived from the original on 2014-05-25. Retrieved 2014-05-25.
  11. By Saharareporters, New York Jan, 29 2014, 9:01AM. Adamawa Bishop Says Boko Haram Killed 31 Of His Parishioners. Archived 2014-05-25 at the Wayback Machine
  12. Sunday, 02 February 2014 05:00. Kabiru R. Anwar, Chakawa death toll rises to 41; pastor killed in fresh Hyambula attack.
  13. Ndahi Marama & Umar Yusuf, January 29, 2014. Adamawa church attack: Death toll rises to 138. Vanguard Nigeria.