Kisan gilla a Kawuri

Harin ƴan ƙungiyar Boko Haram a Kawuri

Kisan gilla na Kawuri ya faru ne a ranar 26 ga watan Janairun 2014 a Kawuri, wani ƙauye a karamar hukumar Konduga mai tazarar kilomita 37 daga kudu maso gabashin Maiduguri a jihar Borno, a arewa maso gabashin Najeriya.

Infotaula d'esdevenimentKisan gilla a Kawuri
Map
 11°34′00″N 13°32′00″E / 11.5667°N 13.5333°E / 11.5667; 13.5333
Iri incident (en) Fassara
aukuwa
Kwanan watan 26 ga Janairu, 2014
Adadin waɗanda suka rasu 85

Hari gyara sashe

Kimanin mahara 50 ne suka kai hari kan fararen hula da bama-bamai da bindigogi. Sun kona gidaje tare da yin garkuwa da mata. Adadin waɗanda suka mutu na karshe ya kai 85. [1] [2] [3]

Ana kyautata zaton maharan sun fito ne daga ƙungiyar ta'adda masu jihadi ta Boko Haram . [4] Ayyukan da suka yi a Konduga sun haɗa da harbe-harbe a 2013, kisan kiyashi a watan Fabrairun 2014, yakin 2014 da 2015, da kuma harin ƙuna baƙin wake a 2018 da 2019.

Manazarta gyara sashe

Coordinates: 11°34′00″N 13°32′00″E / 11.5667°N 13.5333°E / 11.5667; 13.5333