Hadiza Dawaiya Shagari, wacce aka fi sani da Hadiza Shehu Shagari (1940/41 – 12 Agustan 2021) ta kuma kasance jigo a Najeriya, tsohuwar uwargidan shugaban ƙasar Najeriya ce daga shekarar 1979 zuwa 1983, kuma matar Shehu Shagari.[1] Tare da kuma sauran matan Shehu Shagari guda biyu, Hadiza Shagari ta kasance uwargidan shugaban ƙasar Najeriya a lokacin da mijinta ya karɓi shugabancin ƙasar daga 1 ga Oktoban 1979 zuwa 31 ga Disambar 1983.[2][3]

Hadiza Shagari
Rayuwa
ƙasa Najeriya
Mutuwa Abuja, 12 ga Augusta, 2021
Karatu
Harsuna Turanci
Hausa
Sana'a
Sana'a First Lady (en) Fassara

Tarihin Rayuwa

gyara sashe

Hadiza Dawaiya ta haɗu da mijinta, Shehu Shagari, a lokacin da yake aiki a matsayin malami mai ziyara kuma mamba a hukumar bayar da tallafin karatu ta tarayya a lardin Sokoto (jihar Sokoto a yau).[2] Sun yi aure a shekara ta 1957.[2]

Hadiza Shagari ta rasu sakamakon kamuwa da cutar COVID-19 a cibiyar keɓewar Gwagwalada da ke Abuja da misalin ƙarfe 3 na safe a ranar 12 ga watan Agustan 2021.[2][4] Tana da shekaru 80 a duniya.[3] An yi jana'izar ta a babban masallacin ƙasa na Abuja ranar 12 ga watan Agusta da ƙarfe 4[2][4] na yamma Mijinta tsohon shugaban ƙasa Shehu Shagari ya kuma rasu a shekarar 2018.[3]

Manazarta

gyara sashe