Godiya Akwashiki
Godiya Akwashiki (an haife shi ranar uku 3 ga watan Agustan shekara ta alif dari tara da da saba'in da uku miladiyya 1973) a Angba Iggah na Jihar Nasarawa, Najeriya dan siyasar Najeriya ne.[1][2] Shi ne Sanata mai wakiltar Nasarawa ta Arewa a Jihar Nasarawa.[3][1][4] An zabe shi a majalisar dattawa a lokacin babban zaben 2019 na Najeriya. An sake zaben Akwashiki a zaben 2023. Kafin a zabe shi a majalisar dattawa ya kasance mataimakin kakakin majalisar dokokin jihar Nasarawa.[1][5]
Godiya Akwashiki | |
---|---|
mutum | |
Bayanai | |
Bangare na | Sanatocin Najeriya na Majalisar Dokoki ta Kasa ta 9 |
Jinsi | namiji |
Ƙasar asali | Najeriya |
Sunan asali | Godiya Akwashiki |
Sunan haihuwa | Godiya Akwashiki |
Shekarun haihuwa | 3 ga Augusta, 1973 |
Wurin haihuwa | Jahar Nasarawa |
Harsuna | Turanci da Pidgin na Najeriya |
Sana'a | ɗan siyasa |
Muƙamin da ya riƙe | mamba a majalisar dattijai ta Najeriya da mamba a majalisar dattijai ta Najeriya |
Ɗan bangaren siyasa | All Progressives Congress |
Ƙasa | Najeriya |
Personal pronoun (en) | L485 |
Farkon Rayuwa da ilimi
gyara sasheAn haifi Akwashiki a cikin shekarar dubu daya da dari Tara da Saba,in da uku miladiyya 1973 ga Mista Akwashiki Walaro da Mrs Ramatu Akwashiki a Angba Iggah[permanent dead link], ƙaramar hukumar Nasarawa Eggon a jihar Nasarawa.[2] Ya halarci Makarantar Firamare ta Gwamnati, Angba Iggah[permanent dead link] inda ya gama da shaidar kammala karatunsa na farko a cikin shekarar 1987. A cikin shekarar 1988 ya shiga Kwalejin Fasaha ta Gwamnati, Assakio kuma ya kammala karatunsa da Babban Sakandare a Ilimi (WASSCE) a shekara ta 1993.
Akwashiki ya shiga Jami'ar Jihar Nasarawa, Keffi kuma ya kammala karatun digiri na farko a fannin Kasuwancin Kasuwanci a shekara ta 2010. Yana da aure da yara.[6]
Sana'ar Siyasa
gyara sasheDaga shekarar 2011 zuwa 2019, Akwashiki, a ƙarƙashin jam'iyyar People's Democratic Party, ya kasance ɗan majalisar dokokin jihar Nasarawa. A wa'adinsa na farko daga 2011 zuwa 2015 ya kasance shugaban masu rinjaye a Majalisar Jiha.[7] A wa’adinsa na biyu daga 2015 zuwa 2019 an naɗa shi mataimakin kakakin majalisar jiha, muƙamin da ya riƙe har zuwa cikin shekarar 2019, a ƙarƙashin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ya tsaya takarar Sanatan Nasarawa ta Arewa.
A halin yanzu shi ne shugaban kwamitin majalisar dattawa mai kula da harkokin majalisa da kuma mataimakin shugaban kwamitin yaɗa labarai da hulɗa da jama’a.[8]
Manazarta
gyara sashe- ↑ 1.0 1.1 1.2 "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2020-09-23. Retrieved 2023-04-07.
- ↑ 2.0 2.1 https://afripost.ng/2019/12/30/senator-godiya-akwashiki-early-life-education-political-career/
- ↑ https://www.premiumtimesng.com/news/top-news/317358-nigerian-senator-elect-stripped-in-viral-video.html?tztc=1
- ↑ "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2020-05-15. Retrieved 2023-04-07.
- ↑ https://thenationonlineng.net/akwashiki-defeats-mike-abdul-for-nasarawa-norths-seat/
- ↑ https://leadership.ng/
- ↑ "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2020-02-10. Retrieved 2023-04-07.
- ↑ "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2019-12-31. Retrieved 2023-04-07.