Gani Odutokun
Gani Odutokun (Agusta 9, 1946 - Fabrairu 15, 1995) ɗan Najeriya ne mai zane-zane ya shahara wajen ba da gudummawa da kuma renon mawaƙa a cikin al'ummar fasahar a garin Zariya dake a Nigeria. Ayyukansa sun haɗa da Allon bango, zane-zane da ƙirar murfin littafi. [1]
Gani Odutokun | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Ghana, 9 ga Augusta, 1946 |
ƙasa |
Najeriya Ghana |
Mutuwa | 16 ga Faburairu, 1995 |
Yanayin mutuwa | (traffic collision (en) ) |
Karatu | |
Makaranta | Jami'ar Ahmadu Bello |
Harsuna |
Turanci Pidgin na Najeriya |
Sana'a | |
Sana'a | painter (en) da Malami |
Rayuwar farko da ilimi
gyara sasheAn haifi Odutokun a garin Nsawan, dake kasar Ghana, iyayensa kuma ‘yan kabilar Yarbawa ne dake kasar Nigeria ’yan asalin garin Offa ne, Jihar Kwara kuma suke sana’ar koko . [2] Ya yi kuruciyarsa ya kuma girma a yankin Ashanti amma daga baya mahaifinsa ya koma Najeriya bayan harkar kasuwancinsa ta koko tayi kasa. Bayan kammala karatunsa na Sakandare, ya yi aiki a matsayin magatakarda a Kamfanin Brew[3]eries na Najeriya amma tare da kwazo daga abokansa da suka ga hazakarsa, sai ya nemi izinin shiga Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya a shekarar 1972. Ya sauke karatu daga kwalejin tare da digiri na farko da na biyu a Fine Arts a 1975 da 1979. [4] Bayan ya kammala karatunsa na digiri, ya shiga Sashen Fine Arts na ABU a matsayin mataimakin digiri.
Manazarta
gyara sashe- ↑ Ekpo Udo Udoma. No More Boundaries
- ↑ ART-NIGERIA: Gani Odutokun Retrospective Hailed in London
- ↑ Cite error: Invalid
<ref>
tag; no text was provided for refs named:0
- ↑ Edewor U. Nelson (2015). Gani Odutokun’s Dialogue with Mona Lisa: Interrogating Implications of Euro-African Interface. International Journal of Arts and Humanities. IJAH 4(1), S/No 13