Funsho Williams

Ɗan siyasar Najeriya (1948-2006)

Anthony Olufunsho Williams (9 ga Mayun Shekarar 1948 - 27 ga Yuli 2006) ɗan siyasa ne mai tasiri daga jihar Legas kuma tsohon kwamishina a ƙarƙashin mulkin soja na Kanar Olagunsoye Oyinlola a Legas.

Funsho Williams
Rayuwa
Haihuwa Lagos,, 9 Mayu 1948
ƙasa Najeriya
Mutuwa 27 ga Yuli, 2006
Yanayin mutuwa kisan kai
Karatu
Makaranta Cibiyar Fasaha ta New Jersey
Jami'ar jahar Lagos
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa da injiniya
Imani
Jam'iyar siyasa Peoples Democratic Party
Alliance for Democracy (en) Fassara
Ofishin funsho williams

Rayuwar farko

gyara sashe

Funsho Williams ya halarci makarantar Katolika ta St. Paul da ke Ebute Metta sannan yayi karatu a St Gregory's College, Legas.[1] Haka-zalika a shekara ta 1968, ya yi karatu a Jami'ar Legas,[2] ya sami digiri a fannin injiniyan farar hula. Daga nan ya ci gaba da zuwa Cibiyar Fasaha ta New Jersey don yin digiri na biyu.[3]

Aikin gwamnati

gyara sashe

A shekarar 1974, Williams ya dawo Najeriya ya shiga aikin gwamnati na jihar Legas . Ya shafe shekaru 17 yana aikin gine-gine a jihar Legas. Kimanin kashi 70% na tituna da gadoji an gina su ne a ƙarƙashin kulawar sa. Williams ya kasance Babban Sakatare a lokacin da ya bar aikin gwamnati a shekarar 1991.

Ya shiga kasuwanci, amma bai jima ba ya koma aikin gwamnati, a matsayinsa na kwamishinan jihar Legas a ƙarƙashin mulkin Kanar Olagunsoye Oyinlola.

A tsakiyar shekarun 1990, Williams ya yanke shawarar shiga siyasa don ya iya tsara manufofin sa gami da aiwatarwa, maimakon fitar da manufofin kawai-(ba tare da iya aiwatarwa ba). Ya fara shiga jam’iyyar United Nigeria Congress Party (UNCP), amma bayan mutuwar shugabanta Janar Sani Abacha ya koma jam’iyyar Alliance for Democracy (AD).

Bayan wani ɗan lokaci kaɗan, Williams ya sake sauya sheka zuwa jam'iyyar People's Democratic Party (PDP). Sun lashe zaɓen shekarar 2003 ƙarƙashin jagorancin shugaba Olusegun Obasanjo .

Williams ya tsaya sau biyu a baya a zaɓen gwamnan jihar Legas (Gubernatorial). A lokacin gab da rasuwarsa yana fatan a tsayar da shi a matsayin ɗan takarar gwamna na jam’iyyar PDP a jihar Legas. Ya sha alwashin kwace mulki daga hannun jam'iyyar Alliance for Democracy Party.

Williams ya gudanar da shugabanci a kamfanoni da yawa da suka haɗa da:

A ranar 27 ga watan Yulin shekarar 2006, an gano Funsho Williams a daure, an shake shi, kuma aka caka masa wuka, a cikin gidansa da ke Dolphin Estate, Ikoyi, wani yanki na musamman kuma unguwar ma su arziki a birnin Legas.[4]

A ranar 28 ga watan Yulin shekarar 2006, an kama mutane biyu dangane da mutuwarsa. Daya shine manajan yakin neman zaɓensa, ɗayan kuwa Sanata ne kuma tsohon ministan ayyuka, Kingsley Adeseye Ogunlewe . Ogunlewe ya kuma yi fatan zama ɗan takarar gwamna na PDP. [1].

An yi jana'izar Williams a makabartar kotun Victoria da ke Legas.[5] Ya bar matarsa mai suna, Hilda da ƴa'ƴa huɗu.[6]

Don tunawa da shi

gyara sashe

A ranar 26 ga watan Fabrairun shekarar 2007, kimanin watanni bakwai da faruwar lamarin kisan gillar, gwamnan jihar Legas na lokacin, Gwamna Bola Ahmed Tinubu, don karrama fitaccen jarumin nan, ya canza sunan babban titin Western Avenue da ke Legas mafi tsawo kuma fitacciyar babbar hanyar Legas, zuwa sunan Funsho William Avenue.[7] Duk da haka, har yanzu yawancin mutanen Legas sun san sunan titin birnin da tsohon sunan: babbar hanyar Western Avenue.

Manazarta

gyara sashe
  1. Gbenga Adeniji (July 7, 2013). "We feared our father's silence- Funsho William's son". The Punch. Archived from the original on 2015-05-28. Retrieved 2015-03-15.
  2. "Reopen Funsho Williams murder probe, Bode George urges Buhari". Punch Newspapers (in Turanci). 2020-07-28. Retrieved 2022-03-07.
  3. Nigeria: The Man Funso Williams
  4. Tunde Opeseitan (August 13, 2014). "Funsho Williams was strangulated - Pathologist". Daily Independent. Archived from the original on 2015-04-02. Retrieved 2015-03-15.
  5. Chidiebere Onyemaizu. "An Emotional Farewell: Nigerians pay their last tribute to Anthony Olufunso Williams as the slain politician was laid to rest". The Source. Archived from the original on 2015-04-02. Retrieved 2023-04-02.
  6. "BREAKING NEWS: Lagos State PDP Gubernatorial Candidate, Funso Williams Assassinated!". Sahara reporters. July 26, 2006.
  7. Oluwatimilehin, Oyekanmi (February 26, 2007). "Nigeria: Yes! What About Funsho Williams Avenue?". allafrica.com. ThisDay Newspaper.

Hanyoyin haɗi na waje

gyara sashe