Freedom Radio Nigeria
Freedom Radio Nigeria rukuni ne na gidajen rediyo[1] a Arewacin Najeriya. Gidan rediyon yana da hedikwata a cikin jihar Kano. Rukunin ya kunshi gidajen rediyo hudu da suka haɗa da Freedom Radio Kano 99.5 FM, Freedom Radio Dutse 99.5 FM, Freedom Radio Kaduna 92.9 FM da Dala FM Kano 88.5 FM. Freedom Radio Nigeria mallakar dangin Dalhatu ne.[2]
Freedom Radio Nigeria | |
---|---|
Bayanai | |
Iri | Tashar Radio |
Ƙasa | Najeriya |
Harshen amfani | Turanci da Hausa |
Mulki | |
Hedkwata | jahar Kano |
Tarihi | |
Ƙirƙira | 2002 |
freedomradionig.com |
Tarihi.
gyara sasheA 2002, Freedom Radio Kano ta sami lasisi daga Laboratory Film and Production Services Limited, don kafa gidan rediyon mai zaman kanya na farko irinsa a arewacin Najeriya a lokacin da sunan SAVANNAH RADIO KANO.
A ranar 1, ga watan Disamban shekarar 2003, gidan rediyon ya fara watsa shirye-shirye da sunansa na yanzu, Freedom Radio FM.
Freedom Radio ta fara ne da tashar guda daya a cikin jihar Kano, Freedom Radio FM Kano 99.5. Bayan haka a shekarar 2007, gidan rediyon ya faɗaɗa zuwa tashar rukuni bayan ƙaddamar da Freedom Radio Dutse a jihar Jigawa .[3] A shekarar 2011, tashar ta sami lasisin bude wasu tashoshin a Kano, Sokoto, Kaduna, da kuma Maiduguri. A shekarar 2011, aka fara amfani da Dala FM 88.5, a Kano.[4][5] sannan a shekarar 2012, aka bude Freedom Radio Kaduna 92.9.[6][7]
Manazarta.
gyara sashe- ↑ https://freedomradionig.com
- ↑ Sa' Adams, eed K. "A Decade on Air: A History of Freedom Radio 99.5 FM, Kano. 2003–2013" (in Turanci). Cite journal requires
|journal=
(help) - ↑ "Freedom Radio Dutse: Contact Information, Journalists, and Overview | Muck Rack". muckrack.com (in Turanci). Retrieved 2020-09-18.
- ↑ "Dala FM 88.5". myTuner Radio (in Turanci). Retrieved 2020-09-18.
- ↑ Kano, Ibrahim Musa Giginyu (2017-01-22). "Why Kano's Dala FM switched from English to Hausa – Ag, station manager". Daily Trust (in Turanci). Retrieved 2020-09-18.
- ↑ "Freedom Radio Kaduna". OnlineRadioBox.com (in Turanci). Retrieved 2020-09-18.
- ↑ "Freedom Radio Kaduna – Live Online Radio". www.liveonlineradio.net (in Turanci). Retrieved 2020-09-18.