Folarin Balogun
Folarin Jerry Balogun , (an haife shi 3, ga watan Yuli a shekara ta 2001), ya kasance ƙwararren ɗan wasan ƙwallon ƙafa mai wasa a matsayin ɗan wasan gaba a kulub ta Arsenal. An haife shi a ƙasar Amurka, ya wakilci Ingila a matakin wasa na matasan duniya.[1]
Folarin Balogun | |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|
Rayuwa | |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Cikakken suna | Folarin Jolaoluwa Jerry Balogun | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Haihuwa | New York, 3 ga Yuli, 2001 (23 shekaru) | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
ƙasa |
Tarayyar Amurka Birtaniya | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Ƙabila | Yan Najeriya a Amurka | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Karatu | |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Harsuna | Turanci | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Sana'a | |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Sana'a | ɗan wasan ƙwallon ƙafa | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
| |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Muƙami ko ƙwarewa | Ataka | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Tsayi | 1.78 m |
Farkon rayuwa
gyara sasheAn haifi Balogun a New York City kuma anyi hijira dashi zuwa Ingila lokacin yana ɗan shekara biyu, ya girma a London. Iyayensa ƴan'asalin Najeriya ne.
Aiki a kulob
gyara sasheBalogun ya fara aiki a kulub ta Arsenal yana ɗan shekara takwas bayan sun bibiye shi yayin da yake buga wasa a kungiyarsa masu wasa na Sunday League, Aldersbrook. Kafin ya yi nasara da Arsenal, ya yi gwaji tare da abokan hamayyarsu na Arewacin London Tottenham Hotspur kuma ya kusan sanya hannu a dasu.[2][3]
Ya sanya hannu kan kwangilarsa na kwararru a watan Fabrairu a shekara ta( 2019).
A watan Yulin a shekara ta(2020), bayan ya kasa amincewa da sabon kwantiragi da Arsenal, an alakanta shi da barin kungiyar, gami da shirin siyar dashi ga Brentford akan fam miliyan( 8).
Ya fara buga wasansa na farko a gasar cin kofin zakarun Turai a ranar( 29), ga watan Oktoba a shekara ta( 2020), inda ya maye gurbi a minti na (74) a wasan rukuni da Dundalk .
Ya ci kwallon sa ta farko a ranar (26) a watan Nuwamba a shekara ta (2020), a wasan Europa da Molde .
A ranar (26), ga watan Afrilu a shekara ta( 2021), Balogun ya sanya hannu kan sabuwar kwantiragi da kulob din. Balogun ya fara buga wasansa na farko a gasar Firimiya a karawar da suka doke Brentford da ci a ranar (13) ga Agusta (2021).
Aiki a matakin duniya
gyara sasheAn haife shi a Amurka ga iyaye ƴan Najeriya[4] kuma ya girma a Ingila, Balogun ya cancanci wakiltar dukkan ƙasashe uku a matakin ƙasa da ƙasa. Bayan ya buga wa Ingila wasa a matakin 'yan ƙasa ta shekara ta (17 ), kuma ya bayyana a gasar cin kofin ƙwallon ƙafa ta Turai ta' yan ƙasa da shekara(17), na (2018), ya karɓi kira daga ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta U (18), ta Amurka a watan Agusta na shekara ta (2018), don sansanin horo da gasa a cikin Czech. Jamhuriya. Ya buga dukkan wasannin Amurka huɗu a Gasar Matasa ta Václav Ježek kuma ya zira kwallaye biyu. Ya kuma nuna sha’awarsa ta bugawa Najeriya kwallo, duk da ya bayyana cewa yana jin dadin irin salon wasan Ingila wanda yayi daidai da na Arsenal.[5]
A cikin shekara ta (2019), ya bayyana kuma ya zira kwallaye a ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Ingila 'yan ƙasa da shekara (18) a wata gasa a Dubai. A watan Oktoban a shekara ta (2020), ya buga wa Ingila U(20), da Wales .
A ranar( 27 ) , ga watan Agusta( 2021), Balogun ya karɓi kiransa na farko zuwa ƙungiyar U(21), ta Ingila . A ranar (7), ga watan Satumba shekarar ( 2021), ya fara buga wasansa na U(21) na Ingila a matsayin wanda zai maye gurbinsa a lokacin shekarar ( 2023) UEFA Turai Under(21 ) Championship cancantar Kosovo U(21) a filin wasa na MK .
Salon wasa
gyara sasheMartin Keown ya kwatanta Balogun da shahararren ɗan wasan Arsenal, Ian Wright, saboda saurin sa da kuma motsi mai hankali.
Ƙididdigar sana'a
gyara sashe- As of wasannin da ya buga tun 22 Satumba 2021
Kulob | Lokaci | League | Kofin FA | Kofin EFL | Turai | Sauran | Jimlar | |||||||
---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|
Raba | Ayyuka | Goals | Ayyuka | Goals | Ayyuka | Goals | Ayyuka | Goals | Ayyuka | Goals | Ayyuka | Goals | ||
Arsenal U21 | 2018–19 | - | - | - | - | 1 [lower-alpha 1] | 0 | 1 | 0 | |||||
2019–20 | - | - | - | - | 1 | 0 | 1 | 0 | ||||||
2020–21 | - | - | - | - | 2 | 1 | 2 | 1 | ||||||
Jimlar | - | - | - | - | 4 | 1 | 4 | 1 | ||||||
Arsenal | 2020–21 | Premier League | 0 | 0 | 0 | 0 | 1 | 0 | 5 [lower-alpha 2] | 2 | 0 | 0 | 6 | 2 |
2021–22 | Premier League | 2 | 0 | 0 | 0 | 1 | 0 | - | - | 3 | 0 | |||
Jimlar | 2 | 0 | 0 | 0 | 2 | 0 | 5 | 2 | 0 | 0 | 9 | 2 | ||
Jimlar aiki | 2 | 0 | 0 | 0 | 2 | 0 | 5 | 2 | 4 | 1 | 13 | 3 |
Manazarta
gyara sashe
- ↑ "List of Players under Written Contract Registered Between 01/07/2018 and 31/07/2018". The Football Association. p. 4. Archived from the original on 24 October 2019.
- ↑ Okeleji, Oluwashina (21 March 2019). "Nigeria yet to approach Arsenal's Folarin Balogun". BBC News. Retrieved 3 November 2020.
- ↑ "Mikel Arteta sends message to Arsenal contract rebel Folarin Balogun". Metro. London. 30 October 2020. Retrieved 3 November 2020.
- ↑ Critchlow, Dan (15 March 2019). "Folarin Balogun admits he hasn't decided international allegiance: England, USA or Nigeria". Daily Cannon. Belfast. Retrieved 3 November 2020.
- ↑ Karen, Mattias (20 August 2018). "U.S. under-18s call up promising Arsenal prospect Folarin Balogun". ESPN. Retrieved 3 November 2020.
Cite error: <ref>
tags exist for a group named "lower-alpha", but no corresponding <references group="lower-alpha"/>
tag was found