Florence Ita Giwa

Dan siyasar Najeriya

Florence Ita Giwa (an haife ta a ranar 19 ga watan Fabrairu a shekara ta 1946) ’yar siyasan Najeriya ce, wacce ta kasance Sanatan gundumar sanata ta Kuros Ribas ta Kudu ta Jihar Kuros Riba.[1]

Florence Ita Giwa
mamba a majalisar dattijai ta Najeriya

29 Mayu 1999 - ga Yuni, 2003 - Bassey Ewa-Henshaw
District: Cross River South
Rayuwa
Haihuwa Jahar Cross River, 19 ga Faburairu, 1946 (78 shekaru)
ƙasa Najeriya
Harshen uwa Kalabari harshe
Ƴan uwa
Abokiyar zama Dele Giwa
Karatu
Harsuna Turanci
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
Imani
Jam'iyar siyasa Peoples Democratic Party
 
Florence Ita Giwa

Ta yi karatu a makarantar kwalejin kimiyya da fasaha ta Kabul Polytechnic a ƙasar Birtaniya. Ta zama ma'aikaciyar jinya.

Fagen siyasa

gyara sashe

Ita-Giwa ta shiga siyasa sannan ta zama shugabar jam'iyar NRC na jihar Delta . Bayan haka, an zabe ta a matsayin mamba a majalisar wakilai ta tarayya a shekara ta (1992 zuwa 1993), [2] kuma ta kasance mamba a kwamitin raba iko da majalisar wakilai ta shekarar (1994 zuwa 1995) Ta tsunduma cikin harkokin Bakassi, har ta sami laƙabi da "Mama Bakassi". Ita-Giwa an zabe ta a matsayin Sanatan mazabar Kuros Riba ta Kudu a watan Afrilun shekarar (1999) kuma an nada shi kwamitocin kan Dokoki da Ka’idoji, Muhalli, Harkokin Kasashen Waje, Mata, Neja Delta da Drug & Narcotics.

Bayan ficewa daga majalisar dattijai a shekarar ( 2003) ta koma jam'iyyar People's Democratic Party PDP, sannan ta zama Mashawarci na Musamman ga Shugaba Olusegun Obasanjo kan al'amuran Majalisar Kasa.

Jita-jita

gyara sashe

A watan Mayun shekara ta ( 2010) akwai jita-jitar cewa kuɗade sun bace daga asusun Kwamitin Tsugunar da Bakassi, karkashin jagorancin Ita-Giwa, wanda ya nemi Hukumar Yaki da Masu Yiwa Tattalin Arzikin Kasa Ta'annati ta binciki lamarin.

Ita Giwa tayi aiki game da fataucin mutane da bautar da mata.

Lambar yabo

gyara sashe

Ta samu lambar yabo ta OON (Jami'in oda na Nijar) da lambar yabo ta The Sun Lifetime Achievement.

Manazarta

gyara sashe
  1. "Florence Ita-Giwa's commitment". This Day. 8 September 2018. Retrieved 10 May 2019.
  2. Encomium Magazine