Emmanuel Bwacha CON ɗan siyasar Najeriya ne wanda aka zaɓa a matsayin ɗan majalisar dattawa mai wakiltar jihar Taraba ta kudu a jihar Taraba dake arewa maso gabashin Najeriya, a babban zaɓen shekarar dubu biyu sa sha ɗaya 2011. An zaɓe shi a jam'iyyar PDP. An sake zaɓen shi a ƙarƙashin jam’iyyar a zaɓen shekarar dubu biyu da sha biyar 2015.[1] An sake ayyana Bwacha a matsayin wanda ya lashe zaɓen na shekarar dubu biyu da sha tara 2019. a Mazaɓar Taraba ta Kudu a jihar Taraba, Najeriya.[2][3][4]

Emmanuel Bwacha
mamba a majalisar dattijai ta Najeriya

11 ga Yuni, 2019 - 11 ga Yuni, 2023
Darius Ishaku
District: kudancin Jihar Taraba
mamba a majalisar dattijai ta Najeriya

9 ga Yuni, 2015 - 9 ga Yuni, 2019
District: kudancin Jihar Taraba
mamba a majalisar dattijai ta Najeriya

6 ga Yuni, 2011 - 4 ga Yuni, 2015
District: kudancin Jihar Taraba
mamba a majalisar wakilai ta Najeriya,

3 ga Yuni, 2003 - 5 ga Yuni, 2007
Rayuwa
Cikakken suna Emmanuel Bwacha
Haihuwa Donga (Nijeriya), 15 Disamba 1962 (61 shekaru)
ƙasa Najeriya
Karatu
Makaranta Jami'ar Calabar
Harsuna Turanci
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
Imani
Jam'iyar siyasa Peoples Democratic Party

Rayuwar farko, ilimi, da aiki

gyara sashe

An haifi Bwacha a ƙaramar hukumar Donga a jihar Taraba.[5] Yana da Diploma a fannin Gudanar da Jama'a daga Jami'ar Calabar. Ma'aikacin gwamnati, ya taɓa riƙe muƙamin kwamishinan noma na jihar Taraba tsakanin shekarar dubu ɗaya da ɗari tara da casa'in da tara 1999 zuwa shekar dubu biyu da ukku 2003. a gwamnatin Jolly Nyame.[6] An zaɓi Bwacha a matsayin ɗan majalisar wakilai ta tarayya mai wakiltar mazaɓar Donga/Ussa/Takum, daga watan Mayun shekara ta dubu biyu da ukku 2003 zuwa wayan Mayun shekara ta dubu biyu da bakwai 2007.[7] Ya kasance shugaban kwamitin majalisar kan harkokin ƴan sanda.[8] A zaɓen watan Afrilun shekara ta dubu biyu da bakwai 2007 ya sha kaye a zaɓen kujerar Sanata.[6]

Majalisar Dattawan Najeriya

gyara sashe

Danbaba Suntai wanda yafi so, Bwacha ya lashe zaɓen fidda gwani na jam'iyyar PDP na ɗan majalisar dattawan Taraba ta kudu a cikin watan Janairun shekarar dubu biyu da sha ɗaya 2011 ba tare da adawa daga Sanata mai ci Joel Danlami Ikenya ba, wanda ya tsaya takarar gwamna.[9] A ranar tara 9 ga watan Afrilun shekarar dubu biyu da sha ɗaya 2011 ne Bwacha ya samu ƙuri’u har guda 106,172, yayin da Aliyu na jam’iyyar Action Congress of Nigeria (ACN) ya samu ƙuri’u 80,256.[10] Sanata Bwacha shine ɗan takarar gwamna n jam'iyyar APC a jihar Taraba.

Manazarta

gyara sashe
  1. https://guardian.ng/politics/taraba-newcomers-will-be-busy-learning-the-ropes/[permanent dead link]
  2. https://www.xtra.net/news/politics/emmanuel-bwacha-returns-senate-third-time-198283/[permanent dead link]
  3. https://www.channelstv.com/2019/02/28/inec-declares-senator-shuaibu-winner-of-taraba-senatorial-race/
  4. https://www.blueprint.ng/214620-2/
  5. "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2023-03-19. Retrieved 2023-03-19.
  6. 6.0 6.1 https://allafrica.com/stories/200806260397.html
  7. https://web.archive.org/web/20121007194357/http://www.afdevinfo.com/htmlreports/peo/peo_4078.html
  8. https://web.archive.org/web/20110720075247/http://www.thisdaylive.com/articles/in-taraba-jonathan-can-sleep-with-two-eyes-closed/77445/
  9. https://www.nationalaccordnewspaper.com/?option=com_content&view=article&id=193%3Atarabas-senatorial-race-heading-for-the-last-lap&catid=54%3Apolitical-analysis&Itemid=82
  10. https://web.archive.org/web/20110419203046/http://www.inecnigeria.org/downloads/?did=114