Jolly Nyame
Jolly Tavoro Nyame (an haife shi a ranar 25 Disamba 1955) a ƙaramar hukumar Zing ta jihar Taraba a yau ) shi ne gwamnan jihar Taraba a Najeriya daga 29 ga Mayu 1999 zuwa 29 ga Mayu 2007. Ya kuma yi gwamnan jihar daga watan Janairu 1992 zuwa Nuwamba 1993. Shi dan jam’iyyar PDP
Jolly Nyame | |||||
---|---|---|---|---|---|
29 Mayu 1999 - 29 Mayu 2007 ← Bala Nuhu (en) - Danbaba Suntai →
ga Janairu, 1992 - Nuwamba, 1993 ← Adeyemi Afolahan (en) - Yohanna Dickson → | |||||
Rayuwa | |||||
Haihuwa | Zing (Nijeriya), 25 Disamba 1955 (68 shekaru) | ||||
ƙasa | Najeriya | ||||
Karatu | |||||
Harsuna |
Turanci Hausa Pidgin na Najeriya | ||||
Sana'a | |||||
Sana'a | ɗan siyasa | ||||
Imani | |||||
Jam'iyar siyasa | Peoples Democratic Party |
Rayuwar farko
gyara sasheAn haifi Nyame a ranar 25 ga Disamba, 1955 a Zing, jihar Taraba. yayi aikin Firist kuma an naɗa shi Reverend a Cocin United Methodist Church of Nigeria.
Siyasa
gyara sasheNyame ya shiga siyasa ne a shekarar 1991, ya tsaya takarar gwamnan jihar Taraba a 1992 kuma ya yi nasara. Wa’adinsa na gwamna a shekarar 1992 bai dade ba sakamakon kwace mulki da sojoji suka yi. A 1999, Nyame ya tsaya takarar gwamna a jam’iyyar Peoples Democratic Party kuma ya yi nasara. An kuma sake zaɓe shi a shekarar 2003, wanda hakan ya sa ya zama mutum ɗaya tilo da ya lashe zaɓen gwamna sau uku a jihar Taraba. [1]
Tuhumar laifuka
gyara sasheBayan da ya bar ofis a shekarar 2007, Hukumar Yaƙi da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) ta tuhumi Nyame da laifin zamba na Naira biliyan 1.64 a kan tuhume-tuhume arba’in da ɗaya na zamba. A shekarar 2007, Nyame ya amince da karkatar da naira miliyan 180 daga cikin naira miliyan 250 da aka tanadar wa ma’aikatu a jihar Taraba, ya kuma yi tayin dawo da kuɗin. [1]
Hukunci
gyara sasheA ranar 30 ga watan Mayun 2018 ne wata babbar kotun birnin tarayya Abuja ta yanke wa Nyame hukuncin daurin shekaru 14 a gidan yari, mai shari’a Adebukola Banjoko, bisa laifin da ake tuhumarsa da shi. An nemi ya mayar da kudaden da ya karkatar.
A watan Nuwamba 2018, Kotun daukaka kara da ke Abuja ta tabbatar da samunsa da laifuka 29. Sai dai kotun daukaka kara ta sake duba hukuncin da kotun ta yanke, ta kuma yanke masa hukuncin zaman gidan yari na shekaru 5 daban-daban na shekaru 12 da zai yi a lokaci guda maimakon zaman gidan yari na shekara 14 na farko sannan ta umarce shi da ya biya tarar naira miliyan 185. A ranar 7 ga Fabrairu, 2020, Kotun Koli ta tabbatar da hukuncin zaman gidan yari na shekaru 12 tare da jingine tarar da kotuna suka yi masa kan cewa sun yi taurin kai kuma sun aikata ba tare da wani dalili ba.
Afuwa
gyara sasheA ranar 14 ga watan Afrilu ne gwamnatin tarayyar Najeriya tayiwa Joshua Dariye da Jolly Nyame afuwa. Kungiyoyin fararen hula da sauran jama'a sun soki matakin.
kebantacciyar Rayuwa
gyara sasheNyame yana auren Priscilla JT Nyame.
karin bayani
gyara sashe- Jerin Gwamnonin Jihar Taraba