Kungiyan kwallon kafa na Mayakan El-Kanemi wato da turanci 'El-Kanemi Warriors FC', kungiya ce da ke zaune a garin Maiduguri, jihar Borno, Najeriya. Suna buga kwallo a filin wasa na El-Kanemi . Sun kawo karshen kakar wasanninsu ta shekarar 2005 a wasan dab da kammala gasar firemiya ta Najeriya. An kuma sake su zuwa Rukunin Nijeriya 1 a shekarar ta 2007. Sun sake komawa zuwa matakin farko a shekara ta 2012. Sakamakon rikicin Boko Haram, a shekarar 2014 sun kuma yi wasannin gida a Kano. Daga shekarar 2015 zuwa shekarar 2016 sun karhi bakuncin wasannin gidansu a filin wasa na Muhammadu Dikko da ke Katsina kafin su koma Maiduguri da filin wasa na El-Kanemi . A ranar 17 ga watan Oktoba, shekera ta 2017, kulob din ya sanar da tsohon kocin Enugu Rangers, Imama Amapakabo a matsayin sabon kocinsu kan yarjejeniyar shekara daya.
Wannan mukalar bata da Reference (Manazarta) ko daya, ka taimaka ta hanyar samar da Manazarta daga littafi ko yanar gizo, duba wannan shafin domin samun masaniya akan yanda zaka samar da Reference (Manazarta) a cikin wannan mukalar.
. |
- 1991, 1992
- Kashi na biyu na Kasa : 2
- 1991, 2000
- Gasar cin Kofin Kwallan CAF : wasanni 2
- 1992 - Zagaye Na Farko
- 1993 - Semi-final