Edemariam Tsega (An haifeshi a 7 ga watan yuli a shekarar 1939 ya mutu a 1 ga watan janairu 2018) Edemariam Tsega asali dan kasar habasha likita ne kuma masani, shine ya fara gabatar da karatun bayan kammala karatun digiri a bangaren magungunan ciki (internal medicine) a kasar Habasha

Edemariam Tsega
Rayuwa
Haihuwa Gondar, 7 ga Yuli, 1938
ƙasa Habasha
Kanada
Mutuwa Hamilton (en) Fassara, 1 ga Janairu, 2018
Karatu
Makaranta Addis Ababa University (en) Fassara
London School of Hygiene & Tropical Medicine (en) Fassara
McGill University
Lund University (en) Fassara
Sana'a
Sana'a likita
Kyaututtuka

Rayuwa da aiki gyara sashe

Rayuwar farko da ilimi gyara sashe

Edemariam Tsega Teshale an haifeshi a ranar 7 ga watan yuli a shekarar ta alif (1939) a garin Gondar dake kasar Habsha[1] ga Aleqa Tsega Tesgale, malamin Cocin Orthodox na Habasha kuma shugaban bushara na yankunan Bagemdir da Simien [2] da kuma Yètèmegnu Mekonnen daga shekarar ta alif (1919) har zuwa 2013[3]. Ya samu digri na kimiyya a shekarar 1961 daga jamiá'ar Addis Ababa kuma ya zama likita (MDCM) a shekarar ta alif (1965) daga jami'ar McGill.[4][5] Sa'annan ya tafi zuwa kasar UK domin karatu kuma ya kammala karatun daga Makarantar Kiwon Lafiya ta Landan da Magungunan wurare masu zafi (London School of Hygiene and Tropical Medicine) a shekarar (1969) Kafun shekarar (1971) ya sami horo a bangaren likitancin ciki,(internal medcine) da horo a Gastroenterology[4][5][6]

Aiki gyara sashe

Dawowa daga Habasha gyara sashe

A shekarar (1971) Tsega ya dawo Habasha kuma yayi aiki a fakalti na likitanci na jami'ar Addis Abba a matsayin Daraktan na Internist a asibitin Leul Mekonnen da Haile Selasseie. Daga baya, daga shekarar (1974) zuwa (1991) ya zama shugaban Jami'ar Addis Abba a Sashen Magungunan Ciki, kuma ya shiga fakaltin likitanci na AAU a shekarar (1972) in da ya zama cikakken farfesa a shekarar ta alif (1981) wanda ya sa ya zama dan Habasha na farko da ya cimma hakan[6]

A lokacin aikinsa, an nada Tsega a matsayin Shugaban Kwamitin kammala karatun digiri na fannin likitanci kuma memba a mafi yawwan kwamitocin AAU da ma'aikatar lafiya. Ya kasance shugaban kungiyar likitocin Afirka a tsakanin 1989) zuwa 1990, [5] kuma ya zama shugaban kungiyar likitocin Habasha daga shekarar1990 zuwa (1993). [7] A cikin 1991, ya kammala Dakta a bangaren Falsafa a ilimin halittar jiki daga Jami'ar Lund,[6] kuma an ba shi kyautar Binciken Bincike na Gidauniyar Rockefeller a matsayin Farfesa na Ziyara a Jami'ar McGill. Ya kuma zama daya daga cikin yan Diflomasiyya na Hukumar Kula da Magungunan Cikin Gida ta Amurka . [5]Tsakanin shekarar 1992 da 1994, ya kasance shugaban sashen ilimin likitanci,a AAU . [6]

Tsega ya kuma samu mukamai da dama da mambobi a Ma'aikatar Lafiya ta Habasha, Hukumar Kimiyya da Fasaha ta Habasha, Hukumar Ilimi mai zurfi ta Habasha, da kungiyoyin ilimi da kwararru.

Tsawon shekaru 23, Tsega ya yi aiki a matsayin ƙwararren likitan gastroenterologist wanda ke gudanar da bincike na asibiti tare da tallafi daga Hukumar Haɗin gwiwar ci gaban Sweden, Sashen Bincike da Jami'ar Addis Ababa tar da mai da hankali kan cutar hanta ta yau da kullum [8][9] karami[10]da kuma cutar hanta ta kulllum[5][6]Ya kuma koyar da likitancin asibiti, endoscopic da laparoscopic ga mazauna likitoci da dalibai.

Tsega ya samu yabo na gabatar da shirin bayan kammala karatun digiri a cikin Likitanci a Habasha. Ya yi majagaba a fannin ilimin likitanci na Habasha[11] ya kuma horar da ingantattu da kwararrun likitoci a kasar.[4] Ya ba da gudummawa sosai ga jami'ar, ciki har da koyarwa da horar da daliban likitanci da kuma gudanar da bincike a kan ilimin hanta, gastroenterology, da magungunan wurare masu zafi . Ya kuma kafa Asusun Tallafawa don tallafawa horar da likitocin Habasha a fannin likitancin ciki a asibitocin AAU da Habasha.[12]

Tafiya zuwa Kanada gyara sashe

Bayan ya koma Kanada a cikin (1994) Farfesa Edemariam ya yi aiki a matsayin farfesa na likitanci a cikin Faculty of Medicine, da jami'ar Memorial ta Newfoundland, kuma daga baya an nada shi Farfesa Emeritus na likitanci a Fakaltuin koyarda likitanci na Jami'ar McMaster . Ya yi aiki a matsayin babban ƙwararren likita daga shekarar1994 har zuwa 2001 a Grand Falls-Windsor dake kasar, Newfoundland, kuma daga 2001 har zuwa yayi ritaya a 2014 tare da Hamilton Health Sciences / Jami'ar McMaster. [12] [6]Ya ziyarci Habasha sau da yawa na tsawon wata daya don koyarwa a Makarantar Magunguna ta Gondar tsakanin (1999) zuwa 2008.[12]

Tsega ya kasance marubucin wani littafi mai suna The Life History & Qineis na Liqe Kahnat Aleqa Tsega Teshale (mahaifin Tsega) a cikin 2018[13], da jagora don rubuta rahotannin shari'ar likita mai suna Jagoran Rubutun Rahoton Lafiya (Green Book) [14][15]

Rayuwa ta sirri da mutuwa gyara sashe

Tsega ta yi aure a shekarar 1972 da Frances Lester, fitacciyar likita [6].[16] Tare sun haifia yara huɗu, Aida, Naomi, Yohannes da Yodit. [17] 'Yarsa Aida Edemariam, edita kuma marubuci a The Guardian[18], ya buga Labarin Matar: Tarihin Mutum a cikin 2018, [19] wanda shine labarin mahaifiyar Tsega, Yètèmegnu. [20]

Tsega ya mutu a ranar 1 ga Janairu 2018 a Hamilton, Kanada[1].[21] Masu lura da al'amuran kasar Habasha sun bayyana Tsega a matsayin "haske a cikin duhu" da za a rika tunawa da shi a ko da yaushe.[12]

Kyaututtuka da karramawa gyara sashe

Tsega ya sami lambar yabo da yawa da kyaututtuka a duk rayuwarsa, gami da lambar yabo ta Masanin Kimiyya mai Girma daga AAU, Order of the Blue Nile don nasarar kimiyya daga gwamnatin Habasha, lambar yabo ta shugaban kasa don fitattun ayyuka daga Ƙungiyar Ma'aikatan Lafiya, P2P Annual Award in 2004[22], Hamilton Kimiyyar Lafiya, da Kyautar Bikila a 2017. [16][4][23]

An zaɓi Tsega a matsayin ɗan'uwa na Royal College of Physicians and Surgeons of Canada a shekarar 1971,[5] ɗanuwa a World Academy of Sciences a 1987,[24] and danuwa a African Academy of Sciences a 1988.[5]

Nassoshi gyara sashe

  1. 1.0 1.1 "Edemariam Tsega Obituary - Hamilton, ON". Dignity Memorial (in Turanci). 4 January 2018. Archived from the original on 4 April 2023. Retrieved 4 April 2023.
  2. "The Life History & Qineis of Liqe Kahnat Aleqa Tsega Teshale - 978-1-59-907131-2 - Biographies & Memoirs - Book Subjects - by Dr Edemariam Tsega". www.store.tsehaipublishers.com. Archived from the original on 15 June 2021. Retrieved 7 April 2023.
  3. Mohamed, Nadifa (23 February 2018). "The Wife's Tale by Aida Edemariam review – portrait of a mother goddess". The Guardian (in Turanci). ISSN 0261-3077. Archived from the original on 19 March 2023. Retrieved 6 April 2023.
  4. 4.0 4.1 4.2 4.3 "Edemarim Tsega Pioneer in Medicine". Ethiopian Doctors (in Turanci). Archived from the original on 7 April 2023. Retrieved 4 April 2023.
  5. 5.0 5.1 5.2 5.3 5.4 5.5 5.6 "Tsega Edemariam | The AAS". www.aasciences.africa. Archived from the original on 4 April 2023. Retrieved 4 April 2023.
  6. 6.0 6.1 6.2 6.3 6.4 6.5 6.6 Siraj, Elias S.; Darge, Kassa; Tadesse, Yewondwossen (2018). "Edemariam Tsega (1938 – 2018)". International Journal of Ethiopian Studies. 12 (1): 133–136. ISSN 1543-4133. JSTOR 27026542. Archived from the original on 6 April 2023. Retrieved 6 April 2023.
  7. "Prof. Edemariam Tsega". Ethiopian Medical Association (in Turanci). Archived from the original on 4 April 2023. Retrieved 4 April 2023.
  8. Parry, Eldryd; Godfrey, Richard; Mabey, David; Gill, Geoffrey (25 March 2004). Principles of Medicine in Africa (in Turanci). Cambridge University Press. ISBN 978-0-521-80616-9. Archived from the original on 7 April 2023. Retrieved 6 April 2023.
  9. Tsega, Edemariam; Nordenfelt, Erik; Mengesha, Biru; Hansson, Bengt Göran; Tsega, Molla; Lindberg, Johan (January 1990). "Age-specific Prevalence of Hepatitis A Virus Antibody in Ethiopian Children". Scandinavian Journal of Infectious Diseases (in Turanci). 22 (2): 145–148. doi:10.3109/00365549009037894. ISSN 0036-5548. PMID 2356438. Archived from the original on 7 April 2023. Retrieved 6 April 2023.
  10. Tsega, Edemariam; Krawczynski, K.; Hansson, B.-G.; Nordenfelt, E.; Negusse, Y.; Alemu, W.; Bahru, Y. (August 1991). "Outbreak of acute hepatitis E virus infection among military personnel in northern Ethiopia". Journal of Medical Virology (in Turanci). 34 (4): 232–236. doi:10.1002/jmv.1890340407. PMID 1940876. S2CID 22415896.
  11. ፕሮፌሰር እደማርያም ፀጋ ከ1929 እስከ 2010 || Professor Edemariam Tsega 1938 - 2018 (in Turanci), archived from the original on 4 April 2023, retrieved 4 April 2023
  12. 12.0 12.1 12.2 12.3 Observer, Ethiopia (5 January 2018). "A prominent physician and educator, Prof. Edemarim Tsega". Ethiopia Observer (in Turanci). Archived from the original on 4 April 2023. Retrieved 4 April 2023.
  13. "The Life History & Qineis of Liqe Kahnat Aleqa Tsega Te…". Goodreads (in Turanci). Archived from the original on 7 April 2023. Retrieved 6 April 2023.
  14. Biniyam L (25 August 2018). "A guide to writing medical case reports (Green book) by Edemariam Tsega". slideshare.net. Archived from the original on 4 April 2023. Retrieved 4 April 2023.
  15. A guide to writing medical case reports. Addis Ababa University Press. 1978. Archived from the original on 6 April 2023. Retrieved 6 April 2023.
  16. 16.0 16.1 "Bikila Award: Events". www.bikilaaward.org. Archived from the original on 9 May 2021. Retrieved 6 April 2023.
  17. "Professor Edemariam Tsega Passed Away". www.bikilaaward.org. 4 January 2018. Archived from the original on 23 January 2022. Retrieved 6 April 2023.
  18. "Aida Edemariam | The Guardian". the Guardian (in Turanci). Retrieved 7 April 2023.
  19. "The Wife's Tale by Aida Edemariam - 9781538502471". www.bookdepository.com. Retrieved 7 April 2023.
  20. Mohamed, Nadifa (23 February 2018). "The Wife's Tale by Aida Edemariam review – portrait of a mother goddess". The Guardian (in Turanci). ISSN 0261-3077. Retrieved 7 April 2023.
  21. "Edemariam Tsega | AddisNews.net" (in Turanci). Archived from the original on 7 July 2022. Retrieved 6 April 2023.
  22. "Awards - People to People" (in Turanci). 6 February 2022. Archived from the original on 21 January 2023. Retrieved 6 April 2023.
  23. "Bikila Awards for Ethiopian achievers". Ron Fanfair (in Turanci). 4 October 2017. Archived from the original on 4 April 2023. Retrieved 6 April 2023.
  24. Sciences (TWAS), The World Academy of. "Edemariam Tsega". TWAS (in Turanci). Archived from the original on 6 July 2022. Retrieved 6 April 2023.

Hanyoyin haɗi na waje gyara sashe