Eddy Newman
Edward “Eddy” Newman[1] (an haife shi a ranar 14 ga watan Mayu 1953) tsohon ɗan siyasan Biritaniya ne, wanda ya yi aiki a matsayin ɗan Majalisan Tarayyar Turai (MEP).
Newman ya yi aiki da ofishin tura saqonni sannan ya yi aikin injiniyan wutan lantarki. Ya kuma zama mai fafutuka a cikin Jam'iyyar Labour, kuma an zabe shi a Majalisar Birnin Manchester a 1979. A zaben Majalisar Turai na 1984, an zabe shi don wakiltar Greater Manchester Central.[2] Ya kasance memba na Rukunin Kamfen na sashin hagu.[3]
Newman ya kasance kansila na Woodhouse Park a Majalisar Birnin Manchester tun 2002 kuma shine Shugaban Hukumar Rukunin Gidajen Jama'a na Wythenshawe.[4] kuma ya kasance magajin garin Manchester a tsakanin 2017-18. Matar Newman Sheila (an haife ta a shekara ta 1955/56) ita ma yar majalisa ce a cikin birni, mai wakiltar gundumar Chorlton.[1]
Manazarta
gyara sashe- ↑ 1.0 1.1 "Williams, Jennifer (19 February 2018). "Tributes paid to Lady Mayoress of Manchester who has died suddenly". Manchester Evening News. Trinity Mirror. Retrieved 19 February 2018.
- ↑ BBC-Vacher's Biographical Guide 1996. London: BBC Political Research Unit and Vacher's Publications. 1996. pp. 6–29. ISBN 0951520857.
- ↑ Labour's `infantile' tendency barks back". Independent. 15 January 1995. Retrieved 1 February 2015.
- ↑ "Cllr Eddy Newman". Wythenshawe Community Housing Group. Retrieved 1 February 2015.