E9 (ƙasashe)
Taron E9 dai wani taro ne na ƙasashe Tara, wanda aka kafa gamayyar ƙungiyar da ta ƙunshi ƙasashen domin cimma burin shirin UNESCO na Education For All (EFA).[1] "E" (Education) yana nufin ilimi kuma "9" na wakiltar ƙasashe Tara masu zuwa: Bangladesh, Brazil, China, Egypt, India, Indonesia, Mexico, Najeriya da Pakistan, [2] gamayyar ƙungiyar ƙasashen na wakiltar fiye da rabin al'ummar duniya da kashi 70% na daga waɗanda basu iya rubutu da Karatu ba-(illiterate) a duniya.
E9 | |
---|---|
Bayanai | |
Iri | ma'aikata |
Aiki | |
Mamba na | Bangladash, Brazil, Sin, Misra, Indiya, Indonesiya, Mexico, Najeriya da Pakistan |
Tarihi | |
Ƙirƙira | 1993 |
Asali da Manufa
gyara sasheAn ƙaddamar da haɗa-kar E-9 a shekarar 1993 a lokacin taron EFA da ya gudana a birnin New Delhi, Indiya. E-9 ta zama taron ƙasashe don tattauna abubuwan da suka shafi ilimi, musayar kyawawan ayyuka, da kuma sa ido kan ci gaban da ya shafi EFA.
Manufar yunƙurin assasa wannan haɗa-ka ita ce don haɓaka gami da yaɗa ajandar ci gaba mai ɗorewa na buri na 4 na hanyar haifar da saurin canji a cikin tsarin ilimi a wani tsari na uku daga cikin abubuwan da suka fi dacewa da taron Ilimi na Duniya na shekarar 2020: [3]
- Tallafi ga malamai;
- Zuba jari a harkar basira;
- Ƙoƙarin rage gibin da ke tsakanin masu amfani da fasaha da intanet.
Matsayin zamantakewa
gyara sasheƘasashen haɗa-kar E-9 sun sami ci gaba a fannin tattalin arziki. Brazil, China, Indiya, Indonesiya da Mexico su ne mambobin G-20. Mexico memba ce ta OECD, yayin da China yanzu ita ce ta biyu mafi karfin tattalin arziki a duniya. Brazil da Indiya suma sune ƙasashe goma na farko a fannin tattalin arziki. Indonesiya ma tana bunƙasa cikin sauri. A shekarar 1993, ƙasashen E-9 sun ɗauki kaso 16.5% kawai na GDP na duniya. Yanzu, suna wakiltar kusan kashi 30% na GDP na duniya. [4]
Duba kuma
gyara sasheManazarta
gyara sashe- ↑ "E-9 meet begins today, India to lay road map". Hindustan Times. 8 November 2012. Archived from the original on November 8, 2012. Retrieved 22 November 2012.
- ↑ "E9 Initiative". UNESCO. Retrieved 22 November 2012.
- ↑ "Meeting of Education Ministers of E9 Countries". Drishti IAS (in Turanci). Retrieved 2021-05-14.
- ↑ "E-9 Initiative Background". E-9 Initiative. Archived from the original on 6 August 2014. Retrieved 22 November 2012.