Douye Diri

Ɗan siyasar Najeriya, kuma gwamnan jihar Bayelsa mai ci a yanzu.

Douye Diri (An haifeshi ranar 4 ga watan Yuni, 1959). Ɗan siyasa ne, kuma shine gwamnan jihar Bayelsa mai ci a yanzu.[1][2] Ya kasance sanata mai wakiltar Bayelsa ta tsakiya a jihar Bayelsa a majalisar dokokin Najeriya ta 9.[3][4]

Douye Diri
Gwamnan Jihar Bayelsa

14 ga Faburairu, 2020 -
Henry Dickson
mamba a majalisar dattijai ta Najeriya

11 ga Yuni, 2019 - 11 ga Faburairu, 2020
Rayuwa
Cikakken suna Douye Dirir
Haihuwa Bayelsa, 4 ga Yuni, 1959 (64 shekaru)
ƙasa Najeriya
Ƙabila Mutanen Ijaw
Harshen uwa Harshen Ijaw
Karatu
Makaranta University of Port Harcourt (en) Fassara
Matakin karatu Bachelor of Education (en) Fassara
Harsuna Turanci
Harshen Ijaw
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
Imani
Jam'iyar siyasa Peoples Democratic Party

Farkon rayuwa gyara sashe

Douye Diri ya fara karatunsa na farko a makarantar firamare ta Okoro, Sampou, kuma ya kammala a Rev. Proctor Memorial Primary School, Kaiama a shekarar 1977, inda ya samu shaidar kammala karatunsa na farko.[ana buƙatar hujja] Douye ya yi karatu a kwalejin ilimi da ke birnin Port-Harcourt ta jihar Rivers inda ya samu takardar shedar ilimi ta kasa (NCE) a shekarar 1985. Ya kuma halarci jami'ar Port-Harcourt, inda ya samu digiri na farko a fannin ilimi (B. Ed) Kimiyyar Siyasa a 1990.[Ana bukatan hujja]

Siyasa gyara sashe

A ranar 13 ga watan Fabrairun shekarar 2020 ne kotun ƙolin Najeriya ta soke sakamakon zaɓen gwamnan jihar Bayelsa na 2019 bisa hujjar cewa abokin takarar wanda ya lashe zaɓen, David Lyon, ya miƙa takardar shaidar sirri ga hukumar zaɓe mai zaman kanta.[5] Kotun ta umarci a ba Diri takardar shaidar cin zaɓe, wanda zai sa shi zama zaɓaɓɓen gwamna.[6]

A ranar 14 ga Fabrairu 2020 aka rantsar da shi a matsayin gwamnan jihar Bayelsa.[7]

Hukunce-hukuncen kotu, Agusta 2020 gyara sashe

A ranar 17 ga watan Agustan shekarar 2020, wata kotu a Abuja, Najeriya, ta ba da Umar in tsige Diri daga muƙamin gwamnan jihar.[8] Sai dai a ranar 2 ga Oktoba, 2020, wata kotun ɗaukaka kara da ke zamanta a Abuja ta yi watsi da hukuncin wancen kotun tare da tabbatar da shi a matsayin Gwamna.[9][10]

Hayaniya a filin jirgin sama gyara sashe

A watan Agustan 2021, an ba da rahoton cewa Diri da mukarrabansa sun yi tir akan hanyarsu da suka isa dai-dai shingayen bincike na jami’an tsaro a filin jirgin sama na Murtala Muhammed, yayin da suke ƙoƙarin shiga jirgin United Nigeria Airlines na farko daga Legas zuwa Yenagoa.[11]

Manazarta gyara sashe

  1. "Breaking: Douye Diri sworn-in as Governor of Bayelsa". P.M. News. 14 February 2020. Retrieved 14 February 2020.
  2. "Diri and the changing face of Bayelsa - The Nation Newspaper". thenationonlineng.net. Retrieved 2022-02-26.
  3. Iroanusi, QueenEsther (2019-03-11). "INEC releases list of elected senators, APC-62, PDP-37" (in Turanci). Retrieved 2019-08-07.
  4. Bello, Precious (2019-07-11). "Bayelsa guber: Senator Diri joins race". Daily Post Nigeria (in Turanci). Retrieved 2019-08-07.
  5. "Supreme Court Sacks Lyon As Bayelsa Governor-Elect, Hours Before Inauguration". Channels Television. Retrieved 2020-02-13.
  6. Tsa, Godwin (14 November 2019). "Breaking News: Supreme Court sacks Lyon, Bayelsa gov-elect, for presenting running mate with fake qualification". Sun News NG. Retrieved 13 February 2020.
  7. Wahab, Bayo (14 February 2020). "Douye Diri sworn in as Bayelsa Governor". Pulse NG. Retrieved 14 February 2020.
  8. "Tribunal sack Govnor Diri, order fresh election just days afta im bin jubilate say e win case for di same court". BBC News Pidgin. 17 August 2020. Retrieved 2020-08-17.
  9. "Appeal court confam Douye Diri election as Bayelsa Govnor". BBC News Pidgin. Retrieved 2020-10-06.
  10. "Court of Appeal affirms Bayelsa Gov Douye Diri's election". Pulse Nigeria (in Turanci). 2 October 2020. Retrieved 2020-10-06.
  11. ""The Bags Belong To The Governor"—Power-Drunk Bayelsa State Governor, Douye Diri, Aides Breach Airport Security Procedure, Refuse To Be Screened To Board Flight". Sahara Reporters. Archived from the original on 2 September 2021. Retrieved 2 September 2021.