Dorben Polytechnic
Wannan mukalar bata da Reference (Manazarta) ko daya, ka taimaka ta hanyar samar da Manazarta daga littafi ko yanar gizo, duba wannan shafin domin samun masaniya akan yanda zaka samar da Reference (Manazarta) a cikin wannan mukalar.
. |
Dorben Polytechnic, Kwalejin kimiyya da Ƙere-ƙere ce mai zaman kanta wacce Ma'aikatar Ilimi ta Tarayya (FME) da Hukumar Kula da Ilimin Fasaha (NBTE) ta amince da ita a Najeriya, Afirka ta Yamma.
Dorben Polytechnic | |
---|---|
| |
Standard education at it peak | |
Bayanai | |
Iri | polytechnic (en) |
Ƙasa | Najeriya |
Harshen amfani | Turanci |
Tarihi | |
Ƙirƙira | 1995 |
poly.dorben.edu.ng |
Kwalejin Dorben Polytechnic wadda a da ake kiranta (Abuja School of Accountancy and Computer Studies-ASACS) tana Garam, (Garam main campus) Jihar Neja, Najeriya, da wani harabar wajen arewacin Suleja, duka a Jihar Neja. Da can ana kiranta da Dorben Polytechnic (Bwari) Abuja, tunda asalinta tana da babban harabarta/Sashenta a Bwari, Abuja (kuma anan ne aka fara aikin tantancewa). Makaranta ce mai zaman kanta, kwalejin na bayar da horon da zai kai ga ba da lambar yabo ta National Diploma (ND) da Higher Diploma Program (HND) ga ɗaliban da suke da niyyar yin aiki a matsayin akawu, fannin kwamfuta, masu gudanarwa, da manajoji.
Tarihin kafa makarantar
gyara sasheAn kafa ta a cikin shekarar 1995 kuma Hukumar Kula da Ilimin Fasaha ta Kasa da Ma'aikatar Ilimi ta Tarayyar Najeriya ta amince da kuma ba su izinin zama makarantar Ƙere-ƙere a shekarar 1999. Makarantar ta fara da ɗalibai 250 kawai, kamar a shekarar 2010 Dorben tana da ɗalibai sama da 3500 da membobin tsangayyu sama da 45. Kafin a ba makarantar matsayin kwalejin fasaha a shekarar 2007, sai da makarantar ta mallaki kadada (hekta) 50 na fili kuma tana da garantin banki na banki akalla naira miliyan dari da kuma samar da shirye-shiryen injiniyoyi.
A cikin watan Satumba shekarar 2008, ƙungiyar gamayyar ɗalibai ta Najeriya ta bayar da lambar girmamawa ga shugaban kwalejin, Dr A.B Ekwere.