Kuɗi, a inda akafi amfani da Kalmar, tana nufin kowane irin abu da ake amfani dashi a wajen cinikayya ana kiran shi da turanci medium of exchange, musamman waɗanda ke kaiwa da dawowa, kamar Takardun banki da Ƙwandala.[1][2] wani ma'anarsa shine ita wani tsari ne na kudi da ake amfani dasu musamman a cikin kasa.[3] ƘarƘashin wannan ma'anar ne, Dalar Amurka, British pounds, Australian dollars, European euros da Russian ruble duk suka zama misalan kudi ne.[4]

kudi
legal fiction (en) Fassara da medium of exchange (en) Fassara
Bayanai
Ƙaramin ɓangare na legal tender (en) Fassara, nominal good (en) Fassara da standard of deferred payment (en) Fassara
Amfani payment (en) Fassara da trade (en) Fassara
Tarihin maudu'i history of money (en) Fassara
File:Nigeria naira.jpg
kudin najeriya
Kudi da aka yi amfani dasu lokaci Mai tsawo

Hayoyin Samun Kudi Gyara

Akwai hanyoyin da ake samun kuɗi da yawa a duniya, ko a zamanin da bahaushe ya kasance yana da sanao'in gargajiya.

Tun a wancen lokacin ya kasance yana yin su domin ya samu abun dogaro da kai wato idan yayi zai samu kudi imma ta hanyar saida abun ko kuma ta hanyar sashi wani aiki da yayi a biya shi lada, kodai ta hanyar yimasa kyauta ko ya roka a wajen wani.

Ire-iren kudi Gyara

 
Kudin amerika

Kudi yakasu kashi da yawa, cikinsu akwai. kwandaloli(coins), akwai takardar kudi, sannan a zamance akwai kudin yanar gizo-gizo. da sauransu wanda ada, Akanyi amfani da Gishiri ko karfe mai daraja kamar su 'azurfa zinare da Duwatsu masu daraja.

Kudi a Zamanance Gyara

A wannan karnin kuma da muke ciki al'umma sun wayi gari da nau'in kudin yanar gizo dana irgen banki(bank money, awannan zamani akanyi cinikayya batareda da kudi a hannun mai sayan kayaba. Dalilin samun nau'in kudin zamani,muddin akwai katin banki(ATM Card) a hannun mai sayayyan ko kuma na'urar sadarwa kamar komfuta da wayar hannu.

Manazarta Gyara

  1. "Currency". The Free Dictionary.
  2. Bernstein, Peter (2008) [1965]. "4–5". A Primer on Money, Banking and Gold (3rd ed.). Hoboken, NJ: Wiley. ISBN 978-0-470-28758-3. OCLC 233484849.
  3. "Currency". Investopedia.
  4. "Guide to the Financial Markets" (PDF). The Economist.