Colette Sénami Agossou Houeto (an haife ta a shekara ta 1939) Malama ce 'yai ƙasar Benin, mawaƙiya mai fafutukar kare hakkin mata kuma 'yar siyasa. Ta kasance ministar ilimin firamare da sakandare a gwamnatin Boni Yayi na farko.[1]

Colette Sénami Agossou Houeto
Minister of Education of Benin (en) Fassara

Rayuwa
Haihuwa Porto-Novo, 1939 (84/85 shekaru)
ƙasa Benin
Karatu
Makaranta Ludwig Maximilian University of Munich (en) Fassara
University of Strasbourg (en) Fassara
Harsuna Faransanci
Sana'a
Sana'a maiwaƙe, marubuci da ɗan siyasa

An haifi Colette Houeto a cikin shekarar 1939 a Porto-Novo a Sashen Ouémé. Ta halarci makarantun firamare na gida kafin ta tafi makarantar sakandare a Cotonou.[1] Ta halarci Jami'ar Strasbourg kuma daga baya Ludwig Maximilian University of Munich. A Benin ta yi aiki a matsayin Darakta na Cibiyar Horar da Bincike kan Ilimi daga shekarun 1977 zuwa 1981. Ta kuma rubuta kundin wakoki, wanda aka buga a shekarar 1981.[2] Daga shekarun 1986 zuwa 1991, ta yi aiki tare da bankin raya Afirka, da nufin shigar da mata cikin shirin raya ƙasar Benin.[1]

Colette Houeto ta kasance mai fafutuka a Jam'iyyar Sabunta Dimokuradiyya ta Adrien Houngbédji.[1]

  • 'La femme, source de vie dans l'Afrique traditionnelle', in La Civilisation de la femme dans la tradition africaine, Paris: Présence africaine, 1975
  • 'Education et mass-media', Présence Africaine, No. 95 (1975), pp.428-40
  • L'aube sur les cactus. Porto-Novo, Bénin, 1981. Preface by Jean Pliya. Illustrated by Jean-Claude Lespingal.
  • 'Women and Education: the Case of Benin', EDUAFRICA, Vol. 8 (1982), pp.169-179

Manazarta

gyara sashe
  1. 1.0 1.1 1.2 1.3 Mathurin C. Houngnikpo; Samuel Decalo (2013). "Houéto, Colette Senami Agossou". Historical Dictionary of Benin. Rowman & Littlefield. p. 205. ISBN 978-0-8108-7171-7.
  2. University of Western Australia site on Francophone African Women Writers