Cibiyar International des Civilizations Bantu

Cibiyar International des Civilizations Bantu (CICIBA) ƙungiya ce ta al'adu da ke a Libreville, Gabon. An kafa ta ne bisa yunƙurin shugaban ƙasar Gabon Omar Bongo a ranar 8 ga watan Janairu, 1983, an sadaukar da shi ga nazarin al'ummar Bantu.

Cibiyar International des Civilizations Bantu
Bayanai
Farawa 1983
Shafin yanar gizo ciciba.info

A shekarar 2012, an bayyana cewa za a gyara cibiyar bayan watsi da ita a shekarar 1988 saboda rashin kudi.[1]

Kasashe mambobin CICIBA sun hada da Angola, Kamaru, Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, Comoros, Jamhuriyar Kongo, Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo, Equatorial Guinea, Gabon, Ruwanda, São Tomé da Principe, da Zambia.[2]

Manazarta

gyara sashe
  1. "The CICIBA soon to be renovated - Gabonews English" . en.gabonews.com . Archived from the original on 13 December 2013. Retrieved 6 June 2022.
  2. Jeune Afrique (2014-09-03). "Le Centre international des civilisations bantoues, un mirage africain – Jeune Afrique" . JeuneAfrique.com (in French). Archived from the original on 2017-05-19. Retrieved 2020-06-05.

Hanyoyin haɗi na waje

gyara sashe