Chukwuemeka Nwajiuba (an haife shi a ranar 20 ga watan Agusta 1967) ɗan siyasan Najeriya ne kuma lauya. [1] [2] [3] Ya kasance Ƙaramin Ministan Ilimi na Tarayyar Najeriya. [4] [5] daga shekarun 2019 kuma ya yi murabus a ranar 28 ga Afrilu, 2022, bayan da ya karɓi fom ɗin nuna sha'awa da tsayawa takara a jam'iyyar APC don neman Shugabancin Najeriya a zaɓen shekarar 2023 wanda Project Nigeria Group ya bayar. A baya ya taɓa zama Shugaban Hukumar Amintattu ta TETFUnd. [6]

Chukwuemeka Nwajiuba
Minister of State for Education (en) Fassara

21 ga Augusta, 2019 - 11 Mayu 2022
Anthony Anwuka - Goodluck Nanah Opiah (en) Fassara
mamba a majalisar wakilai ta Najeriya,

24 ga Yuli, 2019 - 7 ga Augusta, 2019 - Okafor John (en) Fassara
District: Aguata
mamba a majalisar wakilai ta Najeriya,

11 ga Yuni, 2019 - 24 ga Yuli, 2019
District: Aguata
mamba a majalisar wakilai ta Najeriya,

1999 -
District: Ehime Mbano/Ihite-Uboma/Obowo
Rayuwa
Haihuwa 1967 (57/58 shekaru)
ƙasa Najeriya
Karatu
Makaranta Jami'ar jahar Lagos
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
Imani
Jam'iyar siyasa Accord (Nijeriya)
Peoples Democratic Party
All Progressives Congress

Rayuwar farko da ilimi

gyara sashe

An haifi Nwajiuba a ranar 20 ga watan Agusta 1967 a Umuezeala Nsu a ƙaramar hukumar Ehime Mbano a jihar Imo a kudu maso gabashin Najeriya. Ya karanci Bachelor of Laws (LLB) a Imo State University. Daga nan ya shiga Jami’ar Legas sannan ya kammala digiri na biyu a fannin shari’a (LLM) sannan ya yi digirin digirgir (PhD) a fannin shari’a daga Jami’ar Jos. An kira shi zuwa Bar ta Najeriya a shekarar 1989. [7]

Nwajiuba ya fara aikinsa ne a matsayin babban abokin aikin Ayodeji C. Emeka Ibrahim &Co a shekarar 1991.

Ya tsaya takarar gwamnan Imo a dandalin All People's Party a shekarar 2003, 2007 da 2011. [8] [9] An zaɓe shi ɗan majalisar wakilai a shekarar 1999 – 2003 inda ya zama shugaban kwamitin majalisar wakilai akan filaye, gidaje da ayyuka. [10] [11] [12] Ya kasance memba na jam'iyyar All Progressives Congress kuma sakataren kwamitin tsara kundin tsarin mulki wanda ya samar da kundin tsarin mulki wanda ya haifi All Progressive Congress a shekarar 2013. [13] [14] [15] Ya kasance Shugaban Asusun Tallafawa Manyan Makarantu daga shekarun 2017 zuwa 2019.

An sake zaɓen Nwajiuba ɗan majalisar wakilai ta tarayya ta Okigwe North a shekarar 2019 a ƙarƙashin Accord Party. [16] [17] An zaɓe shi a matsayin minista kuma ya zama ƙaramin ministan ilimi na tarayyar Najeriya a shekarar 2019. [18]

Manazarta

gyara sashe
  1. "Ministerial list: Buhari nominates serving lawmaker who dumped APC". Punch Newspapers. Retrieved 31 August 2019.
  2. "Nwajiuba absolves Buhari of blame on South-East's loss of N'Assembly leadership positions". guardian.ng. Retrieved 31 August 2019.
  3. "I won my first election at 31 –Chukwuemeka Nwajiuba, Minister of State for Education". Punch Newspapers (in Turanci). 2021-09-11. Retrieved 2022-02-22.
  4. "Profile of the Minister of State for Education, Hon. Emeka Nwajiuba". Vanguard News. 21 August 2019. Retrieved 31 August 2019.
  5. "Live Updates: Buhari swears in ministers". Punch Newspapers. Retrieved 31 August 2019.
  6. "House Speakership: Emeka Nwajiuba, The Political Ijele Steps Out". digitaltimesng.com. Archived from the original on 31 August 2019. Retrieved 31 August 2019.
  7. "House Of Reps Speaker: El Rufai's Faction Of Apc Tips Nwajiuba For House Speaker". Nigerian Voice. Retrieved 31 August 2019.
  8. "House Of Reps Speaker: El Rufai's Faction Of Apc Tips Nwajiuba For House Speaker". Nigerian Voice. Retrieved 31 August 2019.
  9. Abuja, Juliana Agbo (16 May 2019). "NASS Speakership: NYCN Makes Case For S'East". Leadership Newspaper. Retrieved 31 August 2019.
  10. "Ministerial list: Buhari nominates serving lawmaker who dumped APC". Punch Newspapers. Retrieved 31 August 2019.
  11. "Chukwuemeka Nwajiuba Archives". 1st for Credible News. Retrieved 31 August 2019.
  12. "House of Reps Speakership: Imo Concerned Citizens rally support for Hon Nwajiuba". Expressive Info. 2 June 2019. Retrieved 31 August 2019.
  13. "NASS leadership: Nwajiuba tasks APC leaders on South-east". Vanguard News. 15 May 2019. Retrieved 31 August 2019.
  14. "Reps' Speakership: Emeka Nwajiuba's Emergence Upsets Gbajabiamila's Ride". ScanNews Nigeria. Retrieved 31 August 2019.
  15. Uzodinma, Emmanuel (31 May 2019). "Reps Speakership: Southeast Leaders, PSC insist on Nwajiuba". Daily Post Nigeria. Retrieved 31 August 2019.
  16. "Emeka Nwajiuba: South East Has Credible Candidates for Speakership Position". Pointblank News. 13 May 2019. Retrieved 31 August 2019.
  17. "Nigeria: INEC alleges sabotage, begs law firms to stop sending junior lawyers to process poll documents". Alternative Africa. 13 May 2019. Archived from the original on 31 August 2019. Retrieved 31 August 2019.
  18. Nyam, Philip (25 July 2019). "Rep lauds Nwajiuba's nomination as minister, want his mandate". Newtelegraph. Archived from the original on 31 August 2019. Retrieved 31 August 2019.