Chu Okongwu
Sonny Chu Okongwu (23 Satumba 1934 – 12 Janairu 2022) masanin tattalin arzikin Najeriya ne kuma ɗan siyasa wanda ya kasance Ministan Tsare-tsare na Ƙasa (1985 – 1986), sannan kuma Ministan Kuɗi (1986 – 1990) a lokacin gwamnatin Babangida.[1]
Chu Okongwu | |||
---|---|---|---|
1986 - 1990 | |||
Rayuwa | |||
Haihuwa | Jahar Anambra, 23 Satumba 1934 | ||
ƙasa | Najeriya | ||
Harshen uwa | Harshen, Ibo | ||
Mutuwa | 12 ga Janairu, 2022 | ||
Karatu | |||
Makaranta |
Jami'ar Harvard Boston University (en) Kwalejin Gwamnati Umuahia | ||
Harsuna |
Turanci Harshen, Ibo Pidgin na Najeriya | ||
Sana'a | |||
Sana'a | Mai tattala arziki |
Rayuwa da aiki
gyara sasheAn haifi Okongwu a ranar 23 ga Satumba 1934 a jihar Anambra, Najeriya. Shi ne na farko a cikin yara takwas. Okongwu ya halarci makarantar St. Michael da ke Aba tsakanin 1941 zuwa 1946. Daga nan ya koma Government College Umuahia, inda ya ke dalibi daga 1947 zuwa 1951. Ya karanta theory of Economic a Boston University, kuma ya kammala digirinsa a 1961. Ya halarci Jami'ar Harvard daga 1961 zuwa 1965.[2][3] Okongwu ya rasu ne a ranar 12 ga Janairu, 2022, yana da shekaru 87.[4]
Manazarta
gyara sashe- ↑ Baffour, Katherine (28 October 2013). "He Was Yoruba, I Am Igbo, But We Were Bosom Friends... - At 79, Sonny Chu Okongwu Reflects On His Life". Naij.
- ↑ "OKONGWU, Dr. Sonny P. Chu". Blerf's Who's Who in Nigeria (Online). Biographical Legacy & Research Foundation. 16 February 2017.
- ↑ Fuady, A. H. (2012). "Elites and economic policies in Indonesia and Nigeria, 1966-1998". Retrieved 20 November 2021. Cite journal requires
|journal=
(help) - ↑ Are, Jesupemi (12 January 2022). "Chu Okongwu, former minister of finance, is dead". The Cable. Retrieved 12 January 2022.