Christopher Oluwole Rotimi (an haife shi a ranar 20, Fabrairu 1935) tsohor Birgediya Janar ne, jami’in diflomasiyya kuma ɗan siyasa mai ritaya, ya yi aiki a lokacin yakin basasar Nijeriya, kuma ya kasance Gwamnan Jihar Yamma a lokacin da Nijeriya ke ƙarƙashin mulkin soja daga 1971 zuwa 1975. Oluwole Rotimi ya zama jakadan Najeriya a Amurka a shekarar 2007.