Chris Olukolade
Chris Olukolade (an haife shi ranar 18 ga watan Maris ɗin 1959). Manjo Janar ne na sojojin Najeriya mai ritaya kuma tsohon Daraktan yaɗa labarai na tsaro. Ya gaji Brig Gen. Mohammed Yerima a ranar 19 ga watan Maris ɗin 2013, kuma Kanar Rabe Abubakar[1][2] ya gaje shi, kafin ya yi ritaya a ranar 30 ga watan Yulin 2015, ya kasance shugaban ƙungiyar masu magana da yawun hukumar tsaro da martani (FOSSRA) a Najeriya.[3]
Chris Olukolade | |
---|---|
mutum | |
Bayanai | |
Jinsi | namiji |
Ƙasar asali | Najeriya |
Suna | Chris |
Shekarun haihuwa | 18 ga Maris, 1959 |
Wurin haihuwa | Idoani (en) |
Harsuna | Turanci, Yarbanci da Pidgin na Najeriya |
Sana'a | soja |
Ilimi a | Jami'ar Tsaron Nijeriya |
Military or police rank (en) | Janar |
Rayuwar farko
gyara sasheMaj. Gen. An haifi Chris Olukolade a ranar 18 ga watan Maris ɗin 1959, a Zariya, Jihar Kaduna ta Arewacin Najeriya amma iyayensa sun fito ne daga Idoani, wani gari a Jihar Ondo, Kudu maso Yammacin Najeriya. Ya samu digiri na farko a fannin fasaha daga Jami’ar Obafemi Awolowo, Ile Ife a cikin shekarar 1983 kuma an ba shi aikin sojan Najeriya a matsayin Laftanar na biyu a shekarar 1982 bisa ga rahoton karatunsa na shekara ta uku a Jami’ar a matsayin sojan Najeriya kuma ɗalibi.[4]
Manazarta
gyara sashe- ↑ https://web.archive.org/web/20160429213114/http://theeagleonline.com.ng/olukolade-becomes-defence-spokesman/
- ↑ https://web.archive.org/web/20160429220014/http://saharareporters.com/2015/07/30/major-general-chris-olukolade-fired-director-defense-information
- ↑ https://web.archive.org/web/20160429223600/http://www.vanguardngr.com/2015/07/general-chris-olukolade-resigns-as-fossra-chairman/
- ↑ https://web.archive.org/web/20160429224733/http://www.premiumtimesng.com/news/more-news/185850-nigerias-defence-spokesperson-olukolade-to-launch-books.html