Cherif Mohamed Aly Aidara
An haifi Cherif Mohamed Aly Aidara a shekarar miladiyya shekarar 1959 a garin Darou Hidjiratou (Dar Al Hijra). Ɗa ne awajen Maimouna Diao ('yace ga Saydou Diao wanda shima sarki ne) da kuma Cherif Al-Hassane Aidara, daga kasar Mauritania, na kabilar “Laghlal” (wanda aka fi sani da Ahlou Cherif Lakhal). Magabatan sa ta layin Cherif Moulaye Idriss, wanda ya kafa daular Idrissid, wanda jinin Hassan ɗan Ali da Fatima yar Annabi Muhammad (Aminci ya tabbata a gareshi).
Cherif Mohamed Aly Aidara | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Darou Hidjiratou (en) , 1959 (64/65 shekaru) |
ƙasa | Senegal |
Karatu | |
Harsuna | Faransanci |
Sana'a | |
Sana'a | shugaban addini |
Imani | |
Addini | Shi'a |
Dan kasa biyu ne, Senegal da Muritaniya.
Cherif ya iya magana, karantu da kuma rubutu da harsuna da dama aciki harda Faransanci, Turanci, Larabci, Wolof da kuma Fulatanci.
Rayuwar sa
gyara sasheCherif shine shugaban al'umman Shia Mozdahir na Afirka da duniya baki daya.
Shi ne Kuma shugaba wanda ya kafa Mozdahir International Insitute (NGO).
Shi ne babban shugaban gidan Radiyon Mozdahir FM da Radiyon Zahra FM na garin Dakar da Kolda yadda yake a jere.
Rubutu da yayi
gyara sasheYa rubuta littattafai akan tauhidin musulunci, tarihin annabi Muhammad (tsira da amincin Allah ya tabbata akanshi) da kuma sahabbai 12 da wasu littattafan, harda:
- Gaskiyar magana akan gadon annabi (Les Vérités de La Succession du Prophète)
- Sayyeda Zaynab (aminci ya tabbata a gareta), gwarzuwan Karbala (Sayyidda Zaynab (paix et salut sur elle) l'héroïne de Karbala)
- Sallolin annabi Muhammad (aminci ya tabbata a gareshi) daka bakin iyalan gidan sa (La prière du Prophète Mouhammad (PSLF) selon les membres de sa famille)
- Ghadir Khum
- Ashura: Ranar jimami ko ranar murna? (Achoura jour de deuil ou jour de fête ?)
- Dokokin harkar kudi na musulunci (Principes de la finance islamique)
Duba sauran wasu abubuwan
gyara sasheManazarta
gyara sashe- APPEL Chérif Mohamed Ali Aïdara, guide des chiites : «Partout dans le monde, les musulmans sont opprimés». Le Quotidien.
- Le chiisme au Sénégal Mozdahir Archived 2020-02-23 at the Wayback Machine. Shia Africa.
- cherif mohamed aly aidara, grand maître au service du peuple et quelques dignitaires Congolais. Daily Motion.
- Chérif Mohamed Aly Aïdara, guide des chiites du Sénégal « Unis, les guides religieux peuvent combattre le terrorisme au Sénégal». Kolda News.
- Institut Mozdahir International Archived 2020-05-08 at the Wayback Machine.
- Sénégal : 127 jeunes de Vélingara s’informent sur l’islam chiite. Shafaqna.
- Chérif Mohamed Aly Aidara, président de Mozdahir International : « L’islam ne peut pas être une religion de violence ». Seneweb.
- Qui est Cherif Mohamed Aly Aidara. Scribd.
- Les pressions faites sur notre communauté ne nous ébranlent point. Enquete Plus.
- Progression du chiisme en Afrique, une donnée qui peut modifier les équilibres géopolitiques. Aleteia.
- Inaugurantion d'une mosquée construite par l’Institut Mozdahir International : Le khalife de Médina Gounass bénit les actions de l’Ong chiite. Leral.
- PORTRAIT – Chérif Aïdara, guide des Chiites : Globe trotter. Le Quotidien.