Bolaji Abdullahi (an haife shi a shekara ta 1969) ɗan siyasan Nijeriya ne kuma Marubuci daga Jihar Kwara . Ya yi aiki a majalisar ministocin tsohon Shugaban kasan Najeriya, Goodluck Jonathan a matsayin mai Girma Ministan Ci gaban Matasa a watan Yulin 2011 sannan daga baya ya zama Ministan Wasanni.[1] Shine marubucin littafin "Sweet Sixteen" wanda JAMB / UTME 2019-2020 ya karba; Da Kuma littafin sa mai suna "Gold-How Jonathan won and lost Nigeria".[2][3]

Bolaji Abdullahi
Minister of Youth Development (en) Fassara

2011 - 2015
Akinlabi Olasunkanmi
Rayuwa
Haihuwa 1969 (54/55 shekaru)
ƙasa Najeriya
Mazauni Ilorin
Harshen uwa Yarbanci
Karatu
Makaranta Jami'ar jahar Lagos
Harsuna Turanci
Yarbanci
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa da ɗan jarida
Imani
Jam'iyar siyasa All Progressives Congress

Farkon Rayuwa da ilimi

gyara sashe

Abdullahi ya kammala digiri da mataki na biyu a fannin ilimin yaɗa labarai daga jami'ar Jihar Lagos a 2001.

A shekarar 1997, Abdullahi ya shiga aikin Jaridar ThisDay a matsayin mai kawo rahoto amma ya bar shekara guda zuwa Taron Shugabancin Afirka. Ya sake dawowa a 2002 inda ya zama Mataimakin Editan Jarida a 2003. Daga baya an nada shi a matsayin Mataimakin na Musamman, Sadarwa da Dabaru ga Gwamnan Jihar Kwara na lokacin, Dokta Bukola Saraki a 2003 sannan daga baya ya zama Mashawarci na Musamman kan Manufofi da Dabaru a 2005. Sannan an nada shi a matsayin Kwamishinan Ilimi, Kimiyya da Fasaha na Jihar Kwara daga 2007 zuwa 2011.[4] Ya ci gaba da aiki a majalisar ministocin tsohon Shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan lokacin da aka nada shi a matsayin Mai Girma Ministan Ci gaban Matasa a watan Yulin 2011 sannan daga baya ya zama Ministan Wasanni.

 
Bolaji Abdullahi

A watan Disambar 2016, an sanar da Abdullahi a matsayin Sakataren Yada Labarai na Jam’iyyar APC . A ranar 1 ga watan Agusta, 2018, a hukumance Abdullahi ya sauka daga mukamin sa na Sakataren Yada Labarai na Jam’iyyar All Progressives Congress ya kuma fice daga jam’iyyar.

Manazarta

gyara sashe
  1. "Bolaji Abdullahi - IDS Alumni, Nigeria". Institute of Development Studies (in Turanci). Retrieved 2018-05-06.
  2. "2023: Ex-Minister, Bolaji Abdullahi, declares for Senate". Punch Newspapers (in Turanci). 2022-02-21. Retrieved 2022-07-24.
  3. "International Youth Day: Associates of Bolaji Abdullahi to hold 'Omoluabi summit'". 30 June 2022.
  4. "Grand 50th Birthday for Former THISDAY Editor, Bolaji – THISDAYLIVE". www.thisdaylive.com. Retrieved 2022-07-24.