Bikin Ranar Nupe biki ne na gargajiya ko al'adu da ake gudanarwa a Najeriya a ranar ashirin da shida 26 ga watan Yuni na kowace shekara. Nupeawa ne ke shirya wannan biki a kowace shekara a ƙasar.[1]

Infotaula d'esdevenimentBikin Ranar Al'adar Nupe
Iri annual event (en) Fassara
biki
Ƙasa Najeriya
Nahiya Afirka
wannan taswirar yankin Nupe ce da ke halartar taron shekara-shekara
bikin ala ada na nufe
kayan Al'adar Nupe

Bikin ranar Nupe rana ce ta gargajiya da kuma shagulgula, wanda ke tuna ranar da Sojojin Burtaniya suka sha kashi a hannun Sojin gargajiya a Afirka ranar ashirin da shida 26 ga watan Yuni shekara ta alif dubu daya da dari takwas da casa'in da shida 1896, lokacin da Masarautar Burtaniya da ke Lokoja ta kusanci sansanin Bida da ke Ogidi na Jihar Kogi ta yanzu wanda ya kawo sakamakon cin nasarar Birtaniyyan da kwace tutar mulkin mallaka na Burtaniya (Union Jack) wanda Sojojin Nupawa suka yi. Dattawan Nupe suka kawo shawarar gudanar da bikin na shekara-shekara, ba kamar bikin Durbar ba da kuma bikin jirgin ruwa na Pategi Ragatta wanda shi ma yana daya daga cikin bukukuwan Nupawa na gargajiya a Arewacin Najeriya.[2][3][4][5]

Ana fara bikin ne da addu'oi a masallatai da cocuka bi da bi a ranakun Lahadi da Juma'a a kowacce ranar farko da kuma ta karshe na bikin, jagoran shine Etsu Yahaya Abubakar wanda shi ne chairman na majalisar sarakunan gargajiya na jihar Neja. A yayin gudanar da bikin ana tattaunawa ka al'adun gargajiya da arziki da kuma hanyoyin bunkasa yawan ƙabilar da kuma tattauna kan maudu'in batutuwan da suka shafi tarihin Nupe, asali, al'adu da ci gabanta sannan kuma suna ba da kyaututtuka masu kyau a ɓangaren noma don inganta aikin noma a garuruwan Nupe.[6][7]

Duba kuma

gyara sashe
  • Bukukuwa a Najeriya

Manazarta

gyara sashe
  1. Dr. Abdullah, Ndagi (12 February 2016). "Nigeria: The Origin of Nupe Day". Leadership Media Nigeria. Retrieved 4 January 2020 – via all Africa.com.
  2. "Nupe Day as tool for cultural revival". PressReader Canada- (Daily Trust Nigeria) published. 2019-06-26. Retrieved 4 January 2020 – via pressreader.com.
  3. Ahmed, Otteh (2019-06-26). "Nupe Day as tool for cultural revival, unity". Daily Trust Newspaper, Nigeria. Archived from the original on 2020-06-29. Retrieved 4 January 2020 – via dailytrust.com.ng.
  4. "Nupes celebrate yet another festival". Vanguard Newspaper. Nigeria. 2010. Retrieved 6 January 2020 – via vanguardngr.com.
  5. "Kulturefest is supporting 37 festivals – Adebiyi". The Punch Newspaper Nigeria. 2016. Retrieved 6 January 2020 – via punchng.com.
  6. "Kulturefest is supporting 37 festivals – Adebiyi". The Punch Newspaper Nigeria. 2016. Retrieved 6 January 2020 – via punchng.com.
  7. "Nupes celebrate yet another festival". Vanguard Newspaper. Nigeria. 2010. Retrieved 6 January 2020 – via vanguardngr.com.