Bennet Ifeakandu Omalu (an haife shi ranar 30 ga watan Satumban shekarar 1968 ) likita ne dan asalin Najeriya mai shaidar zama ɗan ƙasa na Amurka, kuma kwararren likitan jijiyoyi ne wanda shi ne ya fara ganowa da buga sakamakon bincike kan cututtukan ƙwaƙwalwa (CTE) a cikin ’yan wasan ƙwallon ƙafa na Amurka yayin da yake aiki a Gundumar Allegheny ofishin binciken gawa a Pittsburgh. Daga baya ya zama babban mai binciken likitancin na San Joaquin County, California, kuma farfesa ne a Jami'ar California, Davis, sashen likitancin likita da kuma dakin gwaje-gwaje. A yanzu shi ne Shugaba kuma Daraktan Likita na Bennet Omalu Pathology

Bennet Omalu
Rayuwa
Haihuwa Jahar Anambra da Najeriya, Satumba 1968 (56 shekaru)
ƙasa Najeriya
Tarayyar Amurka
Mazauni Lodi (en) Fassara
Karatu
Makaranta University of Pittsburgh (en) Fassara
Jami'ar Najeriya, Nsukka
University of Washington (mul) Fassara
Tepper School of Business (en) Fassara
Harsuna Turanci
Sana'a
Sana'a neuropathologist (en) Fassara, medical examiner (en) Fassara, likita da pathologist (en) Fassara
Employers University of California, Davis (en) Fassara
IMDb nm6013992
bennetomalu.com
Bennet Omalu

Tarihin Rayuwa

gyara sashe

Omalu dan asalin kabilar Igbo ne kuma an haife shi a Nnokwa, Idemili ta Kudu, Anambra a kudu maso gabashin Najeriya a ranar 30 ga Satumbar, 1968, shi ne na shida cikin yara bakwai. An haife shi ne a lokacin yakin basasar Najeriya, wanda yayi sanadiyyar da danginsa suka tsere daga gidansu daga kauyen su na 'yan kabilar Igbo mai suna Enugu-Ukwu a kudu maso gabashin Najeriya. Sun dawo bayan shekara biyu da haihuwar Omalu. Mahaifiyar Omalu tela ce kuma mahaifinsa injiniyan hakar ma'adinai ne kuma shugaban al'umma a Enugu-Ukwu.

Ilimi da Aiki

gyara sashe

Rayuwar Iyali

gyara sashe

Omalu ya auri Prema Mutiso wadda asalin ta 'yar Kenya ce. Suna zaune a Elk Grove, California kuma suna da yara biyu, Ashly da Mark. Ya kasance mai bin addinin Katolika kuma ya samu takardar zama ɗan Amurka a shekarar Fabrairu 2015.  

Manazarta

gyara sashe

Hanyoyin haɗi na waje

gyara sashe