Bashir Usman Tofa ko kuma Bashir Othman Tofa ɗan siyasa ne a Najeriya. Musulmi kuma Kanuri wanda ya taso a birnin Kano, Tofa shi ne ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar National Republican Convention (NRC) a zaɓen da gwamnatin soja ta Ibrahim Babangida ta shirya a shekara ta 1993. Ya rasu a ranar 3 ga Janairun, shekara ta 2022 bayan gajeriyar rashin lafiya.

Bashir Usman Tofa
Rayuwa
Haihuwa jahar Kano, 20 ga Yuni, 1947
ƙasa Najeriya
Mutuwa jahar Kano, 3 ga Janairu, 2021
Karatu
Makaranta London Guildhall University (en) Fassara
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
Imani
Jam'iyar siyasa Babban taron jam'iyyar Republican
Bashir Usman Tofa

Rayuwar sa

gyara sashe

An haifi Bashir Usman tofa a Kano a ranar 20, ga watan Yuni na shekara ta alif ɗari tara da tamanin da bakwai ( 1947) miladiyya. Yayi makarantar firamare ta Shahuci Junior primary school Kano, sai ya cigaba da karatu a makarantar City Senior Primary School a birnin na Kano. Tsakanin shekara ta 1962-1966 ne , ya halarci makarantar Provincial College Kano. Bayan kammala karatu a wannan makarantar ne ya fara aiki da kamfanin Royal Exchange Insurance tsakanin shekara ta 1967-1968. Daga shekara ta 1970 zuwa shekara ta 1973 ya je makarantar City London College Tofa ya shiga harkar siyasa ne a shekara ta 1977 lokacin da yayi Kamsila a mazabar Dawakin Tofa. Sai aka sake zabarsa mamba a majalisar jaha. A jamhuriya ta biyu ne Tofa ya zama sakataren jam'iyyar NPN a jihar Kano har na wasu lokuta. Sannan kuma ya zama sakataren kudi na jam'iyyar .

A jamhuriya ta uku (3) kuma , Tofa ya hade da jam'iyyar NRC a shekara ta 1990. A 1993 lokacin Janar Badamasi Babangida yana shugaban soja a Najeriya ne ya shirya tare da gabatar da tsari OPTION A4, aka zabi Tofa a matsayin dan takarar shugaban kasa mai wakiltar kano kuma ya kayar da Pere Ajunwa da Joe Nwodu da [[Dalhatu] Sarki Tafida] a zaben fidda gwani inda ya dauki tikitin yima jam'iyyar ta NRC takara. Tofa ya yi takara da Sylvesta Ugo a matsayin mataimakin sa.

Tofa yayi rashin nasara a zaben hannun Moshood Kaahimawo Olawole Abiola, bayarbe daga yankin yammacin kasar. Amma daga bisani gwamnatin ta Babangida bata fidda cikakken sakamakon zaɓen ba.

Tofa kuma ɗan kasuwa ne , ɗan kasuwar Mai ne da kuma masana'antu. Shine shugaban kamfanin INTERNATIONAL PETRO-ENERGY COMPANY (IPEC) da kuma ABBA OTHMAN AND SONS LTD. kuma ya zama mamba a kungiyar Century Merchant Bank and General Metal Products.

Ya rasu a ranar 3 ga Janairu shekarar 2022 bayan gajeriyar rashin lafiya.